Matashi Zai Yi Rayuwar Magarkama Bayan Sace Bindiga da Barkonon Tsohuwa a Ofishin ’Yan Sanda

Matashi Zai Yi Rayuwar Magarkama Bayan Sace Bindiga da Barkonon Tsohuwa a Ofishin ’Yan Sanda

  • Wani matashi ya aikata laifin da alkali ya tasa keyarsa magarkama ba tare da beli ko tara ba saboda dalilai
  • Rahoto ya ce matashin ya shiga har ofishin 'yan sanda, inda ya sace bindiga da kuma tulin barkonon tsohuwa
  • Alkali ya ce ba wannan ne karon farko da matashin ya aikata irin wannan laifi ba, don haka ya hukunta shi

Abuja - Wata kotun Dei-Dei dake Abuja, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 21, Joshua Geoffrey, hukuncin daurin shekaru uku a magarkama, bayan kama shi da laifin satar bindiga da barkonon a ofishin jami’an ‘yan sanda.

An tuhumi Geoffrey dake zaune a Kubwa ta babban birnin tarayya Abuja da laifin babbar sata da ta saba doka, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da miji ya kai karar matarsa saboda ya sake ta amma ta ki barin gidansa

Geoffrey dai ya amsa laifinsa, inda ya fashe da kuka tare da neman afuwa da sassaucin alkali.

An daure wani matashin da ya saci bindiga a ofishin 'yan sanda
Matashi Zai Yi Rayuwar Magarkama Bayan Sace Bindiga da Barkonon Tsohuwa a Ofishin ’Yan Sanda | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Yallabai ka yi hakuri, don Allah kada a tura ni magarkama, saboda ba ni da kowa a nan Abuja.
"Don Allah ka yafe min yallabai, ba zan sake aikata kowane irin laifi ba."

Mai shari'a Sulyman Ola ya yanke hukuci, ya ya tura shi magarkama ba tare da zabin biyan tara ba.

Mai shari'a Ola ya ce matashin ba bako bane a aikata laifuka, kuma wannan ne karon farko da aka gurfanar dashi a gaban kotu ba.

Daga nan ya shawarce shi da ya sauya halinsa kana ya zama mutumin kirki idan ya samu damar kammala zaman gidan kaso.

Yadda ya saci bindigar

Mai gabatar da kara, Chinedu Ogada yace matashin ya shiga magarkamar 'yan sanda ne bisa zargin sace wayar salula.

Kara karanta wannan

Ni ba matsiyaci bane: Dan takarar shugaban kasan Najeriya ya ce ya fi shugaban Amurka kudi

Ya ce daga ciro shi daga magarkama domin a share ta, kawai ya yi amfani da damar wajen yin awon gaba da bindiga da barkonon tsohuwa.

Hakazalika, bayanin nasa ya ce, bayan sace bindiga da barkonon tsohuwa, matashin ya sake sace waya da kuma kudi N5,000.

Da yake amsa laifinsa, matashin ya ce ya yi amfani da bindigar ne wajen razana mutane don ya kwaci kudi a hannunsu.

Wani Dan Jihar Anambra Ya Harbe Kaninsa Har Lahira Saboda N1,500 Kudin Wutar Lantarki

A wani labarin, kudin wutar lantarki N1,500 ta hada 'yan uwa biyu fada a jihar Anambra, daya ya fusata ya dirkawa daya bindiga.

Peter Orji ya kashe kaninsa mai suna Godwin ne yayin da gardama ta barke tsakaninsu a gidansu dake Uruagu a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Jaridar Punch ruwaito cewa ’yan uwan biyu suna cikin zaman zamansu ne lokacin da suka fara kai ruwa rana saboda Peter ya ki biyan N1,500 na wuta da yake biya a duk wata.

Kara karanta wannan

Sam: Matashi ya tada kura yayin da yace ba zai ba da hayan matarsa a kan kudi N8.5bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel