Wani Dan Najeriya Ya Ki Tayin N8.5bn, Ya Ce Ba Zai Taba Iya Bada Hayan Matarsa Ba

Wani Dan Najeriya Ya Ki Tayin N8.5bn, Ya Ce Ba Zai Taba Iya Bada Hayan Matarsa Ba

  • Wani dan Najeriya ya tada kura soshiyal midiya bayan ganin wani bidiyon hira da aka yi dashi
  • A faifan bidiyon, an tambaye shi ko zai iya karbar dala miliyan 20 (N8.5bn) domin ba da matarsa haya na mako guda
  • Matashin ya ba da martani mai dumi, lamarin da yasa mutane suka yi ta cece-kuce a kafafen sada zumunta

An tambayi wani matashi wata tambaya mai ban mamaki a wata hirar kan titi, ya ba da amsa mai ban mamaki.

Da aka fara hirar, an tambaye ko zai iya bari matarsa ta kasane da wani na tsawon mako guda shi kuwa a bashi zunzurutun kudi har Naira biliyan 8.5.

Yadda matashi ya ki tayin kudade don ba da hayan matarsa
Wani Dan Najeriya Ya Ki Tayin N8.5bn, Ya Ce Ba Zai Taba Iya Bada Hayan Matarsa Ba | Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Mai tambayan ya ce:

“Idan matarka ta ba ka Naira biliyan 8.5 don ta kasance da wani na tsawon mako guda, wacce amsa za ka bayar?”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba tare da bata lokaci ko dogon tunani ba, nan da nan matashin ya ki amincewa da tayin tare da bayyana cewa ba zai taba amincewa da irin wannan gangancin ba.

Kalli bidiyon:

Batunsa ya jawo martani

Mutane da dama a kafar sada zumunta sun kada baki, sun fadi abin da ke ransu game da matashin.

Ga kadan daga maganganun jama'a:

o_diwurld ya tambaya:

"Amma dai wannan wasa yake? Wannan wane irin wasa ne?"

Ay_oflagosfit yace:

"Oh na ji bazan amince ba, amma zan karba cikin kwanciyar hankali."

shelie456 tace:

"Idan namiji ne zan karba kawai."

Clefbuster1 yace:

"Ka ga kidahumin mutum."

Domnan_ea yace:

"Lallai ma! Bari na karanta martani kawai."

Nakaayijoanitah8 yace:

"Bari na karanta martanin jama'a."

Prince_barry yace:

"Nawa ne kudin kaddara?"

Corsetsteelhome yace:

"Maye dalilin da zai sa ya karba? Idan shi ne zai kwanta da wata mace to tabbas zai karba."

Baba_londoner_backup_ yace:

"Na ma kara masa watanni biyu."

An Hana Shi Shiga Gidan Casu, Ya Yi Aika-Aika, Ya Yanke Wutar Wurin Gaba Daya

A wani labarin, an shiga rudani a wani taron casu da aka hada yayin da wani mutum ya lallaba ta baya ya datse wayar wutar lantarki na dakin taron.

An ce matashin yi wannan aika-aika ne bayan da aka hana shi shiga dakin taron. Maimakon ya koma gida ya ci haushinsa shi kadai, sai ya yanke shawarar daukar fansa.

A wani gajeren faifan bidiyon da aka yada a TikTok, an ga matashin a lokacin da yake datse wayar wutan ta hanyar amfani da karfen yanke wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel