Ni Fa Attajiri Ne, Na Fi Shugaban Kasar Amurka Kudi, Inji Dan Takarar LP Peter Obi

Ni Fa Attajiri Ne, Na Fi Shugaban Kasar Amurka Kudi, Inji Dan Takarar LP Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour ya yi wasu lafuzza dangane da kudaden jihar Anambra a lokacin da yake gwamnan jihar
  • A baya dai Peter Obi ya ce, idan kudaden da ya mallaka na al'umma ne ya sata to kada Allah ya barshi, ya hukunta shi tun a duniya
  • A wannan karon, ya ce shi fa ba talaka bane, domin kuwa yana da kudaden da suka haura na shugaban kasar Amurka Joe Biden

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana asalin dalilin da ya sa ba zai taba iya sace kudin gwamnati ba.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Anambra, Allah ya albarkace shi; don haka ba shi da bukatar satar 'kudin jama'a'.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Peter Obi ya ce ya fi shugaban Amurka kudi
Ni Fa Attajiri Ne, Na Fi Shugaban Kasar Amurka Kudi, Inji Dan Takarar LP Peter Obi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A faifan bidiyon dake yawo a shafin Twitter, Obi ya ce idan ya taba cin kudin al'umma to kada Allah ya bashi natsuwa.

Na fi Joe Biden kudi, inji Obi

Obi ya yi alfahari da cewa ba zai taba kudin al'umma ba, domin Allah ya bashi arziki iya yadda yake bukata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka, Obi ya ce yana wajen lokacin da shugaban kasar Amurka Joe Biden yace yana da kudin da basu wuce $8.9m.

Ya ce shi, a matsayinsa na dan Najeriya kuma kasar da ake ganin mai fama da fatara to ya mallaki abin da shugaban na Amurka bai mallaka ba, don haka ba shi ba sata.

A kalamansa:

"Shugaba Biden ya mallaki dalar Amurka miliyan 8.9, meye yasa wani kamar ni daga wata kasa a duniya ta 3 zai saci kudin jama'a alhali na fi shugaban na Amurka arziki."

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

Ya ce shi ba burinsa bane ya mallaki jirgi mai zaman kasan ko katafaren gida ba, burinsa kawo sauyi ne a Najeriya.

Ku Daina Jiji da Kai, Ku Natsu Ku Kalli Wadanda Kuka Gada, Shawarin Shehu Sani Ga Gwamnoni

A wani labarin, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani ya ba da shawara kyauta ga dukkan gwamnonin Najeriya masu ci.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani wanda yake dan rajin kare hakkin bil-adama ne ya ce duk wani gwamnan da ke jin kansa tamkar sarki ya kamata sake tunani.

A cewar Shehu Sani, gwamnonin da suka sauka daga mulki a baya da yadda suka kare ya ishi wadannan gwamnoni masu ci darasi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel