Hotunan: Haifaffiyar Jihar Kano Ta Zama Lauya A Manyan Kotunan Ingila Da Wales

Hotunan: Haifaffiyar Jihar Kano Ta Zama Lauya A Manyan Kotunan Ingila Da Wales

  • Matashiya Yar Arewa mai suna Munayah Yusuf Hassan, ta zama kwararriyar lauya a manyan kotunan Ingila da Wales
  • An yi bikin karrama Munayah wacce take haifaffiyar yar jihar Kano a ranar Juma'a a birnin Landan
  • Ta zama mace ta farko ‘yar arewacin Najeriya da aka dauka a matsayin kwararriyar Lauya a wadannan kotuna

Ingila - An dauki wata matashiya mai suna Munayah Yusuf Hassan, wacce ta fito daga yankin arewacin Najeriya a matsayin kwararriyar lauya a manyan kotunan Ingila da Wales.

An karrama Munayah ne a wani biki da aka gudanar a ranar Juma’a a birnin Landan, kamar yadda lauya kare hakkin dan adam, Audu Bulama Bukarti ya sanar a shafinsa na Facebook.

Munayah
Hotunan: Haifaffiyar Jihar Kano Ta Zama Lauya A Manyan Kotunan Ingila Da Wales Hoto: AUDU BULAMA BUKARTI
Asali: Facebook

Munayah ta kasance haifaffiyar yar jihar Kano kuma ta kammala karatunta na digiri a jami’ar Bayero da ke Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

Bayan kammala digiri dinta, sai ta zarce makarantar lauyoyi ta Najeriya inda ta zama cikakkiyar lauya kafin ta koma Ingila tare da mijinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto cewa lauyoyin Manyan Kotunan Ingila da Wales suna aiki da bayar da shawarwari da jagoranci ga abokan huldarsu kan dokokin Ingila da Wales.

Hakazalika suna shiga harkokin shari’a da dama kamar dokar kasuwanci, shari’a, dokar iyali da sauransu.

Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe

A wani labarin, wata matashiyar budurwa da ta gaza samun aiki mai kyau bayan kammala karatunta ta bayyana cewa ta shiga damuwa a saboda haka. Bayan dan wani lokaci, ta fara aiki a matsayin mai goge-goge duk da cewar tana da digiri biyu.

Daga nan sai ta fara koyawa wasu dalibai yadda za su yi addu’a da azumi. Budurwar tana kuma karantar da su darusa daga littafi mai tsarki.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Duk da wannan hali da take ciki da kuma kasancewarta mai goge-goge, ta yi tawakkali da Allah sannan ta ci gaba da koyar da kananan yara a hanya madaidaiciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel