Buhari ya Gwangwaje Yayan Uwargidansa da babban Mukami a CBN

Buhari ya Gwangwaje Yayan Uwargidansa da babban Mukami a CBN

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon manajan daraktan kamfanin buga kudi da tsaro na Najeriya, NSPMC
  • An tattaro cewa, sabon daraktan shi ne Ahmed Halilu wanda yayan uwargidansa ne, Aisha Buhari
  • Duk da majiyoyi sun tabbatar da cewa, wannan nadin ya biyo bayan shawararsa Godwin Emefiele, gwamnan CBN ya bai wa shugaban kasan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani rahoto daga jaridar Daily Nigerian ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu matsayin sabon manajan daraktan Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC.

Baba Buhari
Buhari ya Gwangwaje Yayan Uwargidansa da babban Mukami a CBN. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa, Halilu yayan uwargidan shugaban kasa ne, Aisha Buhari.

Amintar shugaban kasan kan nadin Halilu matsayin manajan daraktan kamfanin buga kudin na Najeriya ya biyo bayan shawarar gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Wannan nadin ya zo ne bayan watanni kadan da murabus din Abbas Masanawa, tsohon manajan daraktan NSPMC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, nadin da aka yi wa Halilu zai aiki ne matsayin mukaddashin manajan daraktan bayan shawara ta musamman da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya wanda a halin yanzu shi ne shugaban kwamitin NSPMC Plc.

Waye Ahmed Halilu?

Ahmed Halilu yayan uwargidan shugaban kasa ne wanda yake da gogewar a kalla shekaru ashirin a fannin aikin banki inda ya samu gogewarsa a masana'antu kudi kamar African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank.

Karatunsa ne ya saka shi a sahun gaba na masana a bangaren aikin banki inda yake da digirin farko a fannin noma da kiwo. Yana da digiri na biyu a fannin kasuwanci da wani a fannin huldar kasashen ketare da diflomasiyya duk daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Halilu mamba ne a tsangayar gudanarwa ta NIM.

Buhari ga Gwamnonin APC: Ba Zan Tsoma Baki a Zaben 2023 ba

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya sha alwashin ba zai tsoma kansa ta kowacce siga ba yayin zaben 2023 mai gabatowa, Premium Times ta rahoto.

Yace duk irin shugabancin da aka gina da wani ginshiki daban ba zai amfani kasar ba.

Shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin wasu daga cikin gwamnonin APC a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a gidan gwamnati wacce mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina ya fita a wata takarda kuma yasa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel