Tashin Hankali: Gwamnan PDP Ya Ce Boko Haram Na Shirin Fara Kai Hare-Hare A Jiharsa

Tashin Hankali: Gwamnan PDP Ya Ce Boko Haram Na Shirin Fara Kai Hare-Hare A Jiharsa

  • Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya yi kira ga sabon kwamandan sojoji da aka tura jiharsa ya taimaka wurin magance matsalar tsaro a jihar
  • Yayin jawabin maraba da Birgediya Janar Mohammed Gambo, Fintiri ya ce bayanan sirri da aka kawo masa sun nuna Boko Haram na kokarin kafa sansanin a kananan hukumomi biyu a jihar
  • A baya-bayan nan, dakarun sojoji a Jihar Adamawa sun yi nasarar ragargazan wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram da a Tsaunin Mandara

Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya bukaci sabon kwamandan 23 Armoured Brigade, Birgediya Janar Mohammed Gambo, ya taimakawa jihar magance matsalan tsaron cikin gida.

Birgediya Janar Gambo shine zai maye gurbin Janar A.M. Garba a matsayin kwamanda na 23 Armoured Brigade, bayan sauya-sauyen da babban hafsan sojojin kasa Lt. Janar Yahya Farouq ya yi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC A Abuja

Gwamna Fintiri
Gwamnan PDP Ya Fadi Kananan Hukumomi 2 Da Boko Haram Ke Kokarin Yada Zango A Jiharsa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Fintiri ya kuma bayyana cewa yan kungiyar ta'addanci na Boko Haram suna shirin sake kafa sansaninsu a jihar saboda kai hare-hare, rahoton The Punch.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tarbi sabon kwamandan na 23 Armoured Brigade, yana mai cewa jami'an tsaro suna sa ido kan lamarin don tabbatar da cewa kungiyar ba ta yi nasara ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kananan hukumomi biyu da Boko Haram ke kokarin kafa sansani - Fintiri

A cewar gwamnan, bayanan sirri da aka samu kawo yanzu sun nuna cewa kananan hukumomi biyun da yan ta'addan ke fatan kafa sansaninsu sune Hong da Maiha.

Ya ce yana fatan sabon kwamandan zai taimaka wurin tarwatsa sansanin yan ta'addan.

Cikin jawabinsa gwamnan ya ce:

"Ina tunanin ka zo a lokaci mai muhimmanci, rahoton da ke teburi na ya ce yan Boko Haram na kokarin kafa sansani biyu a jihar, a kananan hukumomin Maiha da Hong.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Gwamnan APC Ya Umurci Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Kamo Masa Wani Sarki A Jiharsa

"Ba ina cewa sun riga sun isa can bane amma dukkan mu mun san akwai alamun suka kokarin kafa sansani a Maiha. An yi kokarin tartwatsa su cikin wata daya zuwa biyu da suka shude.
"Kuma muna sa ido kansu sannan muka kokarin ganin mun tallafawa dukkan hukumomin tsaro don mutanen mu su yi barci da idonsu biyu kuma muna kira gare ku da ke taimake mu magance kallubalen tsaron na cikin gida."

Wannan ne karo na biyu da Gambo ke zuwa aiki a jihar bayan nadin da Lt. Janar Yahya Farouq ya masa, a baya ya taba aiki matsayin kwamanda na 232 battalion.

Takardun bayansa sun nuna ya samu horaswa daban-daban ya kuma yi ayyuka a Najeriya da kasashen waje ciki har da mai sa ido na sojoji a Jamhuriyar Demokradiyya ta Congo.

Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

A wani rahoto, Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, ta ragargaji wasu 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da ke kokarin janyewa juna bayan ba hammata iska a wani yankin jihar Adamawa.

Rundunar sojin ta ce ta samu rakiyar 'yan sa kai na Civilian JTF, inda ta samu bayanai na sirri kan motsin 'yan ta'addan da ya kai ga nasarar hallaka wasu a yau Litinin 21 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel