2023: Binciken EFCC, FBI Kan Zargin Tinubu Da Hannu A Wasu Almundaha Ya Bayyana

2023: Binciken EFCC, FBI Kan Zargin Tinubu Da Hannu A Wasu Almundaha Ya Bayyana

Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC ya bayyana abin da hukumar ta gano bayan bincikar Asiwaju Bola Tinubu
  • Ribadu, a wani rubutu da Joe Igbokwe ya wallafa, ya ce EFCC ba ta samu Tinubu da wani laifi ba a karar da aka kai shi kotu
  • Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawar ya ce ita ma FBI ba ta samu dan takarar shugaban kasar da laifi ba bayan bincikarsa

Joe Igbokwe, na hannun daman Asiwaju Bola Tinuubu, ya binciko abin da Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC ya ce kan tsohon gwamnan lokacin da ya ke shugabantar hukumar yaki da rashawar.

A cewar rubutun da Igbokwe ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ribadu ya ce daya daga cikin jihohin da ya mayar da hankali a kai lokacin yana aiki itace jihar Legas.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki kanin tsohon gwamnan wata jiha, ya tsallake

Bola Tinubu
2023: Binciken EFCC, FBI Kan Zargin Tinubu Da Hannu A Wasu Almundaha Ya Bayyana. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ribadu, a rubutun da Igbokwe ya wallafa, ya ce an fara binciken zargin almundahar kudi a jihar lokacin Tinubu na gwamna.

A lokacin, shugaban na EFCC ya ce ya yi aiki tare da hukumomin tsaro irinsu yan sandan kasa da kasa da hukumar bincike na Amurka (FBI) lokacin da EFCC ba ta samu wani laifi ko abin zargi kan gwamnatin Tinubu ba.

Ribadu ya ce a wannan lokacin sai da ya tuntubi majalisar tarayya da shugabanninta ya ce su jira jami'an tsaron kasashen waje, kuma, a cewarsa, suma ba su samu Tinubu da wani laifi ba.

Ya kara da cewa wannan shine dalilin da yasa jihar Legas kadai a Najeriya ya yi kara a kotu.

Kalamansa:

"Daya daga cikin jihar da muka fi bincika a matsayina na shugaban EFCC itace Legas. Mun aika da bayanai zuwa ga dukkan abokan aikinmu FBI, Metropolitan Police dss.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

"Na tuna lokacin na fada wa majalisar tarayya cewa EFCC bata samu Tinubu da wani laifi ba a Legas. Na ce su jira kasashen waje domin suma suna nasu binciken.
"Dukkan mu muna jiran mu gano rashawa da ake yi a Legas amma har kasashen waje ba su same shi da laifi ba, ba su ga komai ba. Wannan shine dalilin da yasa jihar Legas karkashin Tinubu ce kadai jihar da EFCC ta kai kara kotu..."

Jonathan Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tinubu, Shettima Da Gwamnonin APC A Abuja, Hoto Ya Bayyana

A wani rahoton, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja.

Tinubu ya tafi gidan Jonathan na Abuja ne tare da Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC; Muhammadu Badaru, gwamnan Jigawa; Simon Lalong, gwamnan Plateau, Bello Matawalle, gwamnan Zamfara da wasu gwamnonin.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel