Jonathan Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tinubu, Shettima Da Gwamnonin APC A Abuja, Hoto Ya Bayyana

Jonathan Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tinubu, Shettima Da Gwamnonin APC A Abuja, Hoto Ya Bayyana

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja
  • Tinubu ya gana da Jonathan din ne tare a abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima da wasu gwamnonin APC
  • Ba a bayyana abin da aka tattauna wurin taroon ba duk da cewa ba zai rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023 ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja.

Tinubu ya tafi gidan Jonathan na Abuja ne tare da Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC; Muhammadu Badaru, gwamnan Jigawa; Simon Lalong, gwamnan Plateau, Bello Matawalle, gwamnan Zamfara da wasu gwamnonin.

Jonathan ya gana da Tinubu da Shettima.
Jonathan Ya Saka Labulle Da Tinubu, Shettima Da Gwamnonin APC A Abuja. Hoto: @Imranmuhdz.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

2023: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Dan Takarar Shugaban Kasa Da Obasanjo Ya Ke Goyon Baya

A baya-bayan nan, jiga-jigan APC sun yi kokarin zawarcin tsohon shugaban kasar ya dawo jam'iyyarsu.

A watan Afrilu, magoya bayan tsohon shugaban kasan - wanda dan PDP ne - sun tafi gidansa na Abuja, suna kira gare shi ya fito takara a 2023.

A martaninsa, Jonathan ya ce:

"Kuna kira na in fito takarar a zaben da ke tafe. Ba zan iya fada muku zan yi takara ba. Ba a gama siyasar ba. Ku zuba ido ku gani."

Bayan yan kwanaki, wasu kungiyoyin arewa sun siya wa Jonathan fom din takarar shugaban kasa, amma ya ki karba.

Tsohon shugaban kasar kuma bai tafi wurin tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki ba dama bai taba bayyana cewa ya fita daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ba.

Mutumin da ya nemi ya birkita zaben 2015 saboda Jonathan, ya koma Jam’iyya APC

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Tinubu Ya Sa Labule da Wani Gwamnan Arewa a Abuja

A bangare guda, wani rahoton PM News ya tabbatar da cewa Elder Godsday Peter Orubebe ya sauya-sheka ne bayan abin da ya kira rashin tanadin PDP na karbe mulki.

Da yake yi wa ‘ya ‘yan APC na kasar Ijaw jawabi a ranar Juma’a, 1 ga watan Yuli 2022, ‘dan siyasar ya shaidawa Duniya ya yi rajisa da APC a jihar Delta

Bugu da kari, an rahoto Peter Orubebe yana cewa zai yi wa APC kokari wajen ganin duka ‘yan takaranta biyar sun yi nasara a babban zaben da za ayi a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel