Kanin Tsohon Gwamnan Ekiti, Fayose Ya Tsallake Farmakin ’Yan Bindigan da Suka So Sace Shi

Kanin Tsohon Gwamnan Ekiti, Fayose Ya Tsallake Farmakin ’Yan Bindigan da Suka So Sace Shi

  • Kanin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Isaac Fayose ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka farmake shi
  • Matashin ya yada wani hoto da ke nuna yadda motarsa ta lalace yayin da yake kokarin tserewa barayin
  • Ana yawan samun hare-hare a Najeriya, lamarin da yasa da dama ke damuwa kan yanayin tsaron kasar

Jihar Osun - Yanzu muke samun labarin cewa, wasu 'yan bindiga sun kitsa sace kanin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Isaac Foyose da yammacin ranar Litinin 29 ga watan Agusta.

Fayose ya ba da labarin yadda lamarin ya faru a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa yayin da yake hanyarsa ta zuwa Legas, wasu ‘yan bindiga sun farmaki motarsa tare da yin awon gaba da wasu mutane da ke tafiya daban akan hanyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya Saka Ranar Shari'ar Abba Kyari, Ya Sanar da Lokacin da Za a Dauka

Ya shaida cewa, an sace mutane da dama, shi kuwa ya tsira dakyar, inda ya tsere bayan da suka lalata motarsa.

Yadda 'yan bindiga suka farmaki motar kanin tsohon gwamna
Kanin Tsohon Gwamnan Ekiti, Fayose Ya Tsallake Farmakin ’Yan Bindigan da Suka So Sace Shi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya rubuta cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Nagode wa Allah da ya sa na tsira da rai na!!! Ba a samu asarar rai ba…. An sace wasu da dama.
“'Yan bindiga a yankin Gbogan na jihar Oyo ina zuwa Legas. “Gaskiya babu tsaro a Najeriya ko kadan. Wannan yasa ba zan zabi Tinubu da Atiku ba, su suka sauya Goodluck suka kakaba mana Buhari."

Ba mu san haka ta faru ba

Sai dai, da jaridar Vanguard ta tuntubi hukumar 'yan sandan jihar Osun, rundunar ta ce sam bata samu labarin abinda ya faru ba.

Ta ce sam matashin bai kai rahoto ga 'yan sanda ba, kuma ba lallai su san komai da ke faruwa a kasa ba.

Kara karanta wannan

2023: Ba shan romo yasa nake son gaje Buhari ba, Tinubu ya fadi tanadinsa ga 'yan Najeriya

Hakazalika, hukumar ta ce sam kafar Facebook ba wurin kai koke bane ga 'yan sanda, don haka bata san komai game da hakan ba.

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

A wani labarin, wani mutum dan shekaru 39 mai suna Andy Edwards ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bisa zargin ikrarin shi kyaftin din soja ne a Legas, inda ya iakata fashi da makami.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama matashin a ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hundeyin, ya shaida cewa, wanda aka kamen soja ne bogi, wanda ke fitowa a matsayin mai mai sana'ar talla. Kana yana gayyato 'yan mata da sunan zai dauke su aiki kafin daga bisani ya sace motocinsu ko dan abinda suka zo dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel