Ma'aikatan Lantarki A Najeriya Sun Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Ministan Kwadago Ya Zauna Da Su

Ma'aikatan Lantarki A Najeriya Sun Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Ministan Kwadago Ya Zauna Da Su

  • Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki na Najeriya, NUEE, ta dakatar d yajin aikin da ta fara a yau ranar Laraba na tsawon makonni biyu
  • Dr Chris Ngige, Ministan Kwadago da samar da ayyuka ne ya sanar da hakan bayan taron sulhu da ya yi da kungiyar yana mai cewa sunyi alkawarin dawo da wutan
  • Sai dai kawo yanzu ba a samu sanarwa daga shugabannin kungiyar na NUEE ba game da cigaban da kuma yiwuwar dawo da wutar nan take

Ma'aikatan wutar lantarki na Najeriya da suka shiga yajin aiki da ya janyo dauke wuta a kasar baki daya don neman a biya musu wasu bukatunsu sun yarda za su dawo da wuta ba tare da bata lokaci ba, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Saura shekara 1 a Mulki, Minista Ya Ambaci Dalilin Gaza Cika Alkawarin Lantarki

Kungiyar, a cewar wata sanarwar da ministan kwadago da samar da ayyuka, ya fitar bayan ya zauna da su sun ce za su dawo da wutan yayin da za su jira gwamnatin ta cika musu alƙawurran.

Ma'aikatan Lantarki.
Ma'aikatan Lantarki Sun Yarda Su Dakatar Da Yajin Aikin Tsawon Mako 2 Bayan Ministan Kwadago Yayi Sulhu Da Su. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Ma'aikan lantarkin, a cewar rahoton TVC News sun dakatar da yajin aikin ne bayan Ministan Kwadago na Najeriya ya shiga tsakani ya yi sulhu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan taron sittin da aka yi na tsawon awanni, Ministan Kwadago cikin kunshin sanarwar da ya Kakakin Ma'aikatan, Olajide Oshundun ya fitar yace:

"Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Dr Chris Ngige, ya kawo karshen yakin aikin da kungiyar ma'aikatar wutar lantarki (NUEE) ta fara bayan zaman gaggawa da aka yi tsakanin kungiyar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, da ministan na Kwadago Dr Chris Ngige ya kira

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

"Dr Ngige ya kafa kwamiti da ta kunshi bangarori uku domin duba koken da ma'aikatar lankarkin suka yi da nufin magance su.
"A karshen taron, Sakatare Janar na NUEE, Joe Ajaero, ya tabbatar wa ministan cewa za a dauki dukkan matakai na dawo da wutan a kasar nan take."

A lokacin wallafa wannan rahoton, babu sanarwar a hukumance daga shugabannin kungiyar.

An kuma yi kokarin ji ta bakin shugabannin kungiyar amma ba a yi nasara ba.

Amma wakilin Legit.ng Hausa ya samu ji ta bakin wani ma'aikacin hukumar rarraba wutar lantarki na Kaduna, Abubakar Sidi Baba, don samun karin haske.

Sidi Baba, wanda ya ce ba da yawun hukuma ya yi magana ba ya ce ya samu cikakken bayani game da taron kuma za a dawo da wutan amma sai an jira transifoma da aka kashe su yi 'dumi'.

"Za a dawo da wutan insha Allah kafin 12 na dare, sai an jira manyan transifoma sunyi 'dumi' kafin a kunna," in ji shi.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel