Yan Sanda, Kwastam Da Sojoji Suna Siyan Tramadol Da 'Colorado' Daga Wurin Mu, Dillalin Kwayoyi Suka Yi Ikirari

Yan Sanda, Kwastam Da Sojoji Suna Siyan Tramadol Da 'Colorado' Daga Wurin Mu, Dillalin Kwayoyi Suka Yi Ikirari

  • Dillalan miyagun kwayoyi a wadanda ke sayar da hajojinsu a kusa da tashan jirgin ruwa na Tin Can Island a Legas sun ce jami'an tsaro na cikin kwastomominsu
  • A wani bincike da musamman da aka gudanar, dillalan miyagun kwayoyin sun bayyana farashin da suke sayar da haramtattun kwayoyin da kuma kasashen da ake shigo musu da shi
  • Masana kimiyyar magunguna sun yi tsokaci kan hadarin da ke tattare da ta'amulli da miyagun kwayoyi da kuma hanyoyin da za a bi don magance matsalar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Masu sayar da kwayoyi a kusa da tashan jirgin kasa na Legas sun ce yan sanda da wasu jami'an hukumomin tsaro na cikin wadanda ke siyan kwayoyi irinsu tramdol da 'Colorado' daga 'Loud' daga hannunsu a kan kari.

Binciken da Jaridar Vanguard ta yi ya nuna cewa tashan jirgin ruwa na Apapa da Tin Can Island sun zama wurin da dillalan miyagun kwayoyi ke cin karensu babu babbaka a Apapa, Legas.

Kara karanta wannan

Babu haske: An kammala ganawar gwamnatin Buhari da ASUU, sakamako bai yi dadi ba

Tin Can Islanda Legas.
Jami'an Tsaro Suna Siyan Tramadol Da 'Colorado' Daga Wurin Mu, Dillalin Kwayoyi Suka Yi Ikirari. Hoto: @premiumtimesng.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa jami'an tantance kayayyaki, kwastam, yan sanda da sauran masu amfani da tashan jirgin ruwan na cikin kwastomomin dillalan kwayoyin.

Duk da rushe bukoki da kanguna da aka yi a kusa da tashar jirgin ruwan, har yanzu akwai dillalan miyagun kwayoyi da ke kasuwancinsu a kofar tashar jirgin ruwan da kewaye.

An kuma gano cewa kofar shiga Tin Can na biyu ya zama mafaka ga dillalan kwayoyi da masu ta'amulli da su.

Wakilin Vanguard ya lura cewa da dama cikin dillalan miyagun kwayoyin suna basaja ne matsayin masu sayar da magunguna na yau da kullum kamar maganin ciwon jiki da na kara karfin maza.

Da ya yi batta kama a matsayin kwastoma, wakilin majiyar Legit.ng Hausa ya gano cewa ana boye haramtattun magungunan ne cikin amalanke da ake amfani da su don tallar magunguna ba bisa ka'ida ba a gefen titi.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Wakilin ya gano cewa ana sayar da katin kwayan tramadol mai nauyin 250kg kan N400 sai kuma na ruwa ana sayar da shi N1500. An kuma gano cewa tramadol mai nauyin 500mg ana sayar da shi N3000 duk kati.

Wani dillalin a kofar shiga Tin Can ta biyu ya bayyana cewa fitaccen kwayan da ake kira 'Loud' ana sayar da shi daga N2500 zuwa N3000 cikin karamin leda, bisa bukatar kwastoma.

"Ana sayar da Colorado daga N3000 zuwa N5000 saboda yana wuyan samu kuma kwastoma na bukatarsa."

Da ya ke bayyana kwarewarsa a harkar, a hirarsa da wakilin majiyar Legit.ng Hausa, wani dillali ya ce daga Indiya ake kawo Tramadol yayin da ita kuma Colorado daga Canada ake kawo wa.

Amma, dillalan miyagun kwayoyin sun ce cikin kwastomominsu akwai jami'an da suke aikin sauke kaya, wasu kwastam, yan sanda, sojoji, LASTMA da wasu masu amfani da tashar jirgin ruwa.

Sun ce jami'an tsaron na aika yaransu ba sanye da unifom ba su siya musu miyagun kwayoyin.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

Ya kuma ce suna zuwa su kai kwayoyin zuwa wasu wurare idan an yi yarjejeniya da su.

Daya daga cikinsu ya ce:

"Manyan kwastomominmu sune masu aikin sauke kaya a tashar da ke zuwa da yamma su shakata bayan kammala aiki."

Masana Kimiyyan Magunguna sunyi gargadi game da ta'amuli da kwayoyin

Legit.ng Hausa ta tuntube wasu masana don jin abin da za su ce kan ta'amulli da irin miyagun kwayoyin nan da wasu mutane ke yi.

Abdulrahman Omuya, Masanin Kimiyyan Magunguna mazaunin Jihar Kogi ya yi karin haske kan illolin miyagun kwayoyi irinsu tramadol da yadda za a shawo kan lamarin.

Ya ce shan miyagun kwayoyin na da iloli na zahiri da kuma kwakwalwar bil adama da suka hada da tsananin damuwa, rudewa, mantuwa, lalata hanta, illata koda da huhu da sauransu.

Omuya ya cigaba da cewa hanyar magance matsalar shine wayar da kan mutane kan ilolin ta'amuli da miyagun kwayoyin tare da bada shawarwari na kwararru wato 'counselling'.

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

"Kuma yana da kyau masu ruwa da tsaki su kara kokari wurin ganin haramtattun kwayoyi ba su shigowa kasar," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164