'Yan Sanda Sun Kama Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane a Jihar Benuwai

'Yan Sanda Sun Kama Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane a Jihar Benuwai

  • Yan sanda sun yi ram da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane wanda ya shahara a sace mata a Makurdi, jihar Benuwai
  • Gwamnatin jihar ta rushe gidan tsohon shugaban Alƙalai, wanda aka gano waɗan da ake zargin na mafaka a ciki
  • Kakakin yan sanda ta ce dama kwamishina ya yi alƙawarin kama shi bayan kama yaransa biyu makon da ya gabata

Benue - Dakarun yan sanda sun yi ram da Achobo Samuel, hatsabibin mai garkuwa da mutane wanda ya shahara a sace mata a birnin Makurdi, na jihar Benuwai.

Tribune ta tattaro cewa yayin nuna wanda ake zargim a hedkwatar hukumar yan sandan jihar ranar Litinin, kakakin hukumar, Cathrine Anene, ta ce ƙasurgumin ya shiga hannu ne kwana biyu bayan cafke yaransa.

Achobo Samuel.
'Yan Sanda Sun Kama Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane a Jihar Benuwai Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin tsere wa lokacin da dakarun Operation Zenda suka mamaye Mafakarsa a wani gida da ake alaƙanta shi da tsohon shugaban Alƙalai, marigayi Iorhemen Hwande

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

"Idan zaku iya tuna wa biyu daga cikin mambobin tawagarsa sun shiga hannu a maɓoyarsu makon da ya gabata kuma sun amsa laifun su."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yau kuma Dakarun Operation Zenda sun cafke shugaban su idan baku mance da kwamishinan yan sanda ya yi alƙawarin kama shi kuma yanzu ya cika, tuni ya amsa laifin da ake tuhumarsa."

- Anene

Menene alaƙarsa da tsohon shugaban Alƙalai?

Mutumin ya faɗa wa yan jarida cewa mata na da saukin sace wa kuma ya yi takaicin zama sanadin rushe gidan tsohon shugaban Alƙalai, Marigayi Mai Shari'a Iorhemen Hwande, wansa ya kira da kawunsa.

"Na fara kasuwancin garkuwa da mutane bara, mu uku ne ragowar mutum biyun an kama su, Amma na yi dana sanin abinda na yi musamman rushe gidan kawu na."

Legit.ng Hausa ta gano cewa gwamnatin Benuwai ta rushe gida mai ɗakuna huɗu mai alaƙa da tsohon shugaban alƙalan jihar, inda mutanen ke rayuwa suna ƙulla muggan nufin su.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

A wani labarin kuma Jiragen NAF sun yi ruwan wuta kan tulin yan ta'adda a jihohin arewa biyu

Hukumar sojin sama ta Najeriya NAF ta ce jami'anta sun yi nasara kan yan ta'adda a samame da suka kai mafakarsu a Neja.

Hakan ya zo ne awanni bayan gamayyar sojojin sama da ƙasa sun kewaye tare da halaka tulin yan ta'adda a yankin jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel