Sojoji Sun Yi Luguden Wuta a Sansanonin Yan Bindiga a Jihohin Arewa Biyu

Sojoji Sun Yi Luguden Wuta a Sansanonin Yan Bindiga a Jihohin Arewa Biyu

  • Hukumar sojin sama ta Najeriya NAF ta ce jami'anta sun yi nasara kan yan ta'adda a samame da suka kai mafakarsu a Neja
  • Hakan ya zo ne awanni bayan gamayyar sojojin sama da ƙasa sun kewaye tare da halaka tulin yan ta'adda a yankin jihar Kaduna
  • Ga dukkan alamu sojoji sun zafafa kai samame a yaƙin da suke da ta'addanci kuma hakan na haifar da ɗa mai ido

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ƙarshen makon nan, Jami'an hukumar sojin sama (NAF) sun halaka dandazon ƴan ta'adda a wani ruwan wuta ta sama da suka yi kan mafakar su a jihohin Kaduna da Neja.

Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce Jirgin yaƙin NAF ya kai samame kan yan ta'addan da suka taru a ƙauyen Kurebe, ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja biyo bayan bayanan sirrin da aka samu.

Kara karanta wannan

Aminu Duniya: Jiragen Yakin NAF Sun Dagargaza Kwamandan Boko Haram a Niger da Daruruwan Mukarrabansa

Jirgin NAF.
Sojoji Sun Yi Luguden Wuta a Sansanonin Yan Bindiga a Jihohin Arewa Biyu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanan sun tabbatar da cewa yan ta'addan sun tattaru a wurin domin gudanar da wani muhimmin taro karakashin hatsabibin ɗan ta'adda, Aminu Duniya, kwamandan ƙungiyar Boko Haram.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin NAF ya ce a bayanan da suka tattara, Duniya ne ya gayyaci yan ta'addan zuwa mafakarsa da ke Kurebe domin gudanar da taro, sai dai gayyatar ta jawo hankalin yan ta'adda da yawa waɗan da suka isa wurin a kan Babura.

Ya ce:

"Samamen jirgin ya kare cikin nasara kuma ya yi ajalin yan ta'adda da yawa, sai dai babu tabbacin ko Aminu Duniya na cikin waɗan da suka sheƙa barzahu."
"Mun gano cewa Kurebe maɓoyar yan ta'adda ne sabida da daɗewa mazauna yankin sun yi gudun hijira sanadiyyar harin yan bindiga tun shekarar 2021."

Mun samu irin wannan nasara a Kaduna - NAF

Mai magana da yawun NAF ya ƙara da cewa samamen Kurebe na zuwa ne awanni bayan Sojojin sama da ƙasa sun kashe gomman yan ta'adda a yankin Damba a Galbi, ƙaramar hukumar Chikun a Kaduna.

Kara karanta wannan

Abun tausayi: Fasinjan Jirgin Ƙasan Kaduna Ya faɗi Manyan Ayyuka Biyu da Yan Ta'adda Suka Sanya Su

Gabkwet ya ce:

"Mun samu wasu bayanan sirri da suka nuna cewa yan ta'adda na shirin mamaye ƙauyukan da ke kusa, hukumar Soji sai ta ga wannan dama ce da zata basu mamaki idan sun tsinci kansu a lahira."
"Yayin da dakarun soji suka kewaye yankin, an umarci jirgin NAF ya fara zuwa wurin da ake zargi, daga nan aka kaddamar da hari kan su. An tabbatar yan ta'adda da yawa sun mutu."

A wani labarin kuma Fasinjan Jirgin ƙasan Kaduna ya bayyana yadda yan ta'adɗa ke musu wa'azi da Alƙur'ani a sansanin su

Masu garkuwa damu sun rinka mana wa'azin da ƙara mana kwarin guiwar yin addu'a a sansanin su, inji Fasinjan da ya kuɓuta.

Hassan Aliyu, ya ce su kan jawo ayoyin Alƙur'ani yayin da suke magana, ya labarta wani musu da suka taɓa yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel