Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

  • Nyesom Wike da Newgent Ekamon sun dauki hayar Lauya, sun shigar da kara a kotun tarayya
  • ‘Yan jam’iyyar ta PDP sun kalubalanci sakamakon zaben fitar da gwani da PDP ta shirya a Abuja
  • Wike yana ganin Aminu Tambuwal ya sallamawa Atiku Abubakar kuri’unsa ne bayan fara zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamna Nyesom Wike ya na karar ‘dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Jaridar Punch ta kawo rahoto a ranar Juma’a, 12 ga watan Agusta 2022 cewa Gwamnan Ribas ya shigar da kara a babban kotu tarayya a Abuja.

Nyesom Wike da wani jagora a PDP, Newgent Ekamon suka shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 a game da rikicin takaran 2023.

Gazette tace Wike da Newgent Ekamon su na tuhumar jam’iyyar PDP, hukumar INEC, Aminu Tambuwal da Atiku Abubakar a kan zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

‘Yan Takara Sun Dauko ta da zafi, Sun yi wa Atiku Abubakar alkawarin Kuri’u Miliyan 20

Abin da ya faru a zaben tsaida gwani

A zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa da PDP ta shirya, sai a mintin karshe aka ji Gwamna Aminu Tambuwal ya marawa Atiku Abubakar baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka gayyaci Tambuwal ya yi jawabinsa, sai ya umarci magoya bayansa su zabi Atiku. Wasu na ganin wannan ya hana Wike samun tikitin PDP.

Atiku da Tambuwal
'Dan takaran PDP, Atiku da Tambuwal Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

A karshen zaben, Atiku ya samu kuri’a 371, yayin da Gwamna Wike ya tashi da kuri’u 237. Tun bayan lokacin aka samu rabuwar kai tsakanin bangarorin.

Karar da aka kai gaban kotu

A karar da aka shigar, Wike da abokin kararsa sun nemi kotu ta raba gardama ko kuri’un Tambuwal za su iya komawa wajen Atiku a zaben na PDP.

Lauyoyin da suka kai kara sun nemi Alkali ya yi fashin baki kan makomar kuri’un Tambuwal, ganin ya janye takara a lokacin da an fara kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Shiga Kamfe, APC ta Canza Tikitin ‘Yan takarar Gwamnan jihar Katsina

Rahoton da aka fitar yace Lauyoyi na rokon kotu ta ruguza nasarar da Atiku Abubakar ya samu, idan ta tabbata Tambuwal ya fita daga takarar.

A cire sunan Atiku, a sa Wike

Masu karar sun kuma nemi hukumar INEC ta cire sunan Atiku Abubakar daga cikin ‘yan takara.

A karshe, an roki kotun tarayyar ta tsaida Nyesom Wike a matsayin wanda ya lashe zaben gwani na shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa da za ayi.

Za a ba Atiku tarin kuri'u

Wadanda suka shiga neman tikitin zama ‘Yan Majalisa za su marawa Atiku Abubakar baya a 2023. Idan za a tuna, dazu mu ka kawo wannan labari.

Kungiyar ‘Yan takaran Majalisar Tarayyan na PDP sun yi wa Atiku alkawarin kuri’u miliyan 20, amma a tarihin zaben Najeriya, ba a taba samun irin haka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel