Saboda Tsaro: Ku Guji Gidajen Karuwai Da Mashaya, IGP Ya Gargadi Jami’an Yan Sanda

Saboda Tsaro: Ku Guji Gidajen Karuwai Da Mashaya, IGP Ya Gargadi Jami’an Yan Sanda

  • Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya yi gagarumin jan hankali ga jami;ansa a fadin kasar nan
  • IGP Alkali ya gargadi yan sanda a kan su guji ziyarar gidajen karuwai da mashaya saboda gudun kada miyagu su farmake su
  • Shugaban yan sandan ya kuma shawarce su da su zamo masu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cike da kwarewa

Gombe - Babban sufeto janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya shawarci Jami’an yan sandan kasar da su guji zuwa gidajen karuwai da mashaya don guje ma hare-haren miyagu.

Alkali ya bayar da shawarar ne yayin da yake jawabi ya Jami’an rundunar a Gombe yayin rangadin da ya yi a jihar.

A cewarsa, Jami’an yan sanda na cikin hatsari a yanzu, saboda suna samun barazana daga mayakan IPOB, Boko Haram, ISWAP, yan fashi da makami, masu garkuwa da matane da sauransu, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke Tsakanin Kungiyar Yarbawa Na OPC Da Dillalan Shanu A Jihar Kwara

Sufeto Janar na yan sanda
Saboda Tsaro: Ku Guji Gidajen Karuwai Da Mashaya, IGP Ya Gargadi Jami’an Yan Sanda Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya bukace su da su kasance masu lura da tsaro ta hanyar gujema irin wadannan wurare don kada migayu su far masu cikin sauki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban yan sandan yayin da yake kira ga jami’ansa da su dunga gudanar lamuransu cike da kwarewa ya hanyar bin doka da sanin kan aikinsu, ya yi gargadin cewa karbar na goro a wajen al’umma na da tsattsauran hukunci.

“Karbar cin hanci babban laifi ne. Yana da tsananin sosai kuma daidai yake da fashi da makami. Don haka ba zai yiwu mu kasance da yan fashi da makami a tsakaninmu ba, ko kuma kasancewa da dan fashi sanye da kayan yan sanda. Ya zama dole ki zamo masu nagarta, ya zama dole ku zama kwararru.”

Shugaban yan sandan wanda ya bayyana cewa a kwanakin baya ne aka kori wasu jami’an saboda karbar na goro da kuma rashin da’a, ya bayyana kudurin ‘yan sandan da ke karkashinsa na horar da jami’an ‘yan sanda domin inganta ayyukansu.

Kara karanta wannan

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Kwallon Najeriya Mata Guda Shida a Edo

A wani labarin, wasu yan kwallo mata a Najeriya masu tasowa sun shiga hannun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne ranar Jummu'a a yankin Uronigbe, ƙaramar hukumar Orhiomwon, jihar Edo.

Tribune Online ta rahoto cewa an yi garkuwa da yan kwallon mata ne a wani gari da ke iyaka tsakanin jihohin Delta da Edo yayin da suke kan hanyar komawa gida bayan halartar wata gasar kwallo a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel