Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya

Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya

  • Wani matashi ya hangi wani bature da kyakkyawar matarsa bakar fata kwance a bakin hanya
  • A cikin bidiyon mai ban dariya, mutumin ya bukaci masoyan da su murmusa, inda suka amsa tayinsa
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun yi martani, da dama sun nuna muradinsu na son samun soyayya ta gaskiya

Bidiyon wani bature da kyakkyawar masoyiyarsa bakar fata ya yadu a shafukan soshiyal midiya bayan wani matashi ya wallafa shi a TikTok.

Ga dukkan alamu, ma’auratan sun sha fama sun gaji a wannan ranar don haka suka kwanta don su huta a bakin hanya.

Masoya
Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya Hoto:@oluprivv
Asali: UGC

Wani matashi mai suna Olu Privv ya hangi masoyan biyu sannan ya tunkaresu a cikin wani bidiyo mai ban dariya a kan TikTok.

Ya nemi masoyan da su dan murmusa inda suka yi kamar yadda ya bukata cikin yanayi mai ban sha’awa. Harma kyakkyawar matar ta washe fararan hakoranta.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu amfani da TikTok sun yi martani a kan bidiyon

Bidiyon ya haifar da martani a TikTok inda mutane suka bayyana ra’ayoyinsu game da lamarin.

Yayin da wasu mutane ke fatan samun soyayya, wasu na neman sanin dalilin da yasa ma’auratan suka zabi hutawa a bakin hanya.

@khemzpriv.1 ya ce:

“Soyayya na da dadi.”

@choijangmi ta ce:

“Ko kwabo ba a siyar da soyayya. Kawai na ji dadi ganin wadannan mutanen a haka. Kowa ya cancanci a so shi.”

@rkelsey0 ya ce:

“Idan mutum ya fada tarkon soyayya komai ma daidai yake kallonsa a kowani hali.”

@zibaby237 ta ce:

“A ina ne nan? Ya kamata nima na je na nemi masoyina.”

@fakade_sibalkhulu ta ce:

“Basu yi kama da marasa galihu ba watakila suna jiran mota ne kawai.”

Kara karanta wannan

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

Kalli bidiyon a kasa:

Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin, Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin hotunan yadda wata matashiya ta sauya gaba daya bayan ta yi aure da sahibinta.

Matar mai suna Juliet ta je shafinta na TikTok don wallafa wani tsohon hotonta don nuna yadda kamanninta suke a lokacin da take sabuwar amarya.

Fatar jikin Juliet na da dan duhu kuma bata da jiki a hoton. Sai dai kuma, sabon hotonta ya nuna yadda ta sauya gaba daya ta kara wani irin kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel