Rashin Tsaro: IGP Ya Umarci a Zagaye Babban Birnin Tarayya Abuja da Tulin Jami’an Tsaro

Rashin Tsaro: IGP Ya Umarci a Zagaye Babban Birnin Tarayya Abuja da Tulin Jami’an Tsaro

  • Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya ba da umarnin kara yawan jami'ai da ke aiki a zagayen babban birnin tarayya Abuja
  • An samu aukuwar wasu hare-haren 'yan ta'adda a babban birnin kasar, lamarin da ya tono batutuwa na baranzanar tsaro
  • IGP ya kuma ba jama'ar da ke zama a Abuja tabbacin zaman lafiya da kwanciyar hankali a irin kokarin da hukumar ke yi

Abuja - A wani yunkuri na kawar da fargabar mazauna Abuja dangane da barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya ba da umarnin tura karin jami’an ‘yan sanda masu yawan gaske zuwa birnin.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an dauki matakin ne domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna, muhimman kadarorin kasa da dai sauran ababe a zagayen birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ana ta batun hana acaba, FRSC za ta fara kame wasu nau'ikan babura a Najeriya

IGP ya umarci a kara yawan jami'an tsaron Abuja
Rashin tsaro: IGP ya umarci zagaye babban birnin tarayya Abuja da tulin jami'an tsaro | Hoto: topnaija.com
Asali: UGC

IGP ya ba da wannan umarni ne a yayin taron da rundunar ta gudanar a ofishinsa, yayin da yake samun cikakken bayani kan harkokin tsaro a kasar.

Haka kuma ya umarci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da sashen ayyuka, DIG Bala Zama Senchi, da ya sa ido tare da gudanar da umarnin domin tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kula da sauran jihohi

Hakazalika, ya ce yana bukatar irin wannan kula jihohi da ke kewayen Abuja da ke fuskantar barazanar hare-hare daga tsagerun 'yan bindiga, rahoton Channels Tv.

IGP, ya ja kunnen jama’a, musamman ‘yan jarida, kan illolin yada labaran karya, bayanan bogi, da kuma gurbatattun zantuka domin za su iya yin illa ga tsaron kasa.

Hakazalika, ya bai wa ‘yan Najeriya gaba daya, musamman mazauna babban birnin tarayya tabbacin tabbatar da tsaron su da dukiyoyinsu, kana ya bukace su da su gudanar da ayyukansu na halal ba tare da fargabar wani hari ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna Abuja suka dage dole Buhari ya sauke ministansa da mai ba shi shawara

Ya kuma nanata kudurin shugabancin ‘yan sanda na ci gaba da lalubo hanyoyin inganta tsaro a kasar, ta hanyar tattara bayanan sirri, tura ma'aikata da kuma amfani da fasahohin zamani don dakile ayyukan 'yan ta'adda a fadin kasar.

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

A wani labarin, a yau ne biyar daga cikin fasinjojin da ke hannun 'yan bindigan da suka farmaki jirgin Abuja zuwa Kaduna suka kubuta bayan shafe watanni a maboyar 'yan ta'adda.

Daya daga cikinsu ya bayyana irin wahalar da ya sha a hannun 'yan ta'addan, inda ya labarta wani lokaci da aka harbe shi a kasan cibiyarsa amma Allah yasa kwanansa na gaba.

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Facebook na Ibrahim Sheme, mutanen da suka tsira sun ba da tarihin zamansu a sansanin 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel