Jami’an Amotekun Sun Kara Kama yan Arewacin Najeriya 151 Cunkushe Cikin Tireloli Biyu

Jami’an Amotekun Sun Kara Kama yan Arewacin Najeriya 151 Cunkushe Cikin Tireloli Biyu

  • Kungiyar tsaro ta kudu maso yammacin Najeriya Amotekun ta sanar da kara kama wasu matasa daga Arewacin Najeriya guda 151
  • Yan Arewan da hukumar Amotekun ta kama a kudu sunce sun yan cirani ne dake neman halal a yankin
  • Kwamandan Amotekun Adetunji Adeleye ya ce sun samu layu da hotuna da ke nuna alamar samun horo na musamman daga yan Arewan da suka kama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ondo - Kungiyar tsaro ta kudu maso yammacin Najeriya Amotekun ta sanar da kara kama wasu matasa daga Arewacin Najeriya guda 151. Rahoton BBC

Amotekun ta ce ana zargin matasan da kasancewa 'yan ta'addan dake neman yin kutse da samun mafaka yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Amma matasan sun musanta haka, inda suka bayyana kansu a matsayin yan cirani da suka shigo yankin kudu dan neman hallaliyar su.

Kara karanta wannan

Baiwa ce daga Allah: Hoton mata masu tsawon rai da kakar kakarsu ke da rai ya janyo cece-kuce

Mutanen wanda adadin su ya kai 151, kamar yadda kwamandan rundunar ta Amotekun Adetunji Adeleye ya sanar, ya ce sun fito ne daga yankin Arewa maso Yamma daga jihohin Katsina, Kano da Jigawa.

Amotekun
Jami’an Amotekun Sun Kara Kama yan Arewacin Najeriya 151 Cunkushe Cikin Tireloli Biyu FOTO IDOMA VOICE
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adetunji Adeleye ya ce an kama su da layu da hotuna da ke nuna alamar samun horo na musamman.

Ya ce, an tare motocin ne a kusa da hanyar Sango da Akure zuwa Ado, na jihar Ondo.

An kama mata biyar a cikin wadanda ake zargin, sun boya a bayan buhunan wake da shinkafa a cikin tireloli biyu a lokacin da jami'an Amotekun suka tsananta bincike.

Idan aka tuna batya Legit.NG ta rawaito labrin yadda kungiyar Amotekun ta ayi amai ta lashe inda ta bayyana cewa, babu dan ta’adda guda daya a cikin matafiya yan Arewa 170 da ta kama a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa

Amotekun ta ce binciken dan ta gudanar akan su yasa ta gano manoma ne da za su sauka a garin Ogere na Jihar Ogun,

Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Bayan Sun Lakada Mishi Dukan Tsiya A Legas

A wani labari kuma, Wasu fusatattun sojoji sun lakada wa wani dan sanda duka inda suka kashe har lahira a wani hari da suka kai kan babbar hanyar Mile 2 Badagry a jihar Legas a ranar Laraba. Rahoton Daily Trust

Dan sandan da ya rasu ya kasance Insifeto ne da ke aiki da sashen Ojo na rundunar ‘yan sandan jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel