NBC Ta Ci Aminiya Tarar Naira Miliyan 5 Saboda Bidiyon Tona Asirin Yan Bindiga

NBC Ta Ci Aminiya Tarar Naira Miliyan 5 Saboda Bidiyon Tona Asirin Yan Bindiga

  • Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin na Najeriya ta ci kafar watsa labarai ta Trust TV (Aminiya) tarar Naira miliyan 5 saboda bidiyon yan bindiga da ta ce ya saba dokokinta
  • Bidiyon mai dauke da rahotanni na hakika daga yan bindiga, masanna da kwararru a bangaren tsaro da kuma mutanen da harin yan bindiga ya shafa ya tada kura a shafukan sada zumunta
  • A bangaren ta, gidan jaridar ta Trust TV ta ce tana nazarin takardar tarar amma ta ce bata wallafa bidiyon don kambama yan bindiga ba sai dai don wayar da kan mutane da masu ruwa da tsaki na nufin a gano hanyoyin magance matsalar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar Kula da kafafen watsa labarai ta Najeriya, NBC, ta ci gidan watsa labarai na Trust Television Network (Trust TV) tarar Naira miliyan 5 kan bidiyon da ta wallafa mai taken "Nigeria's Banditry: The Inside Story" wanda aka fitar a ranar 5 ga watan Maris na 2022.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Amintattun Jam'iyya Sun Bullo Da Sabuwar Hanyar Rarrashin Gwamna Wike da Wasu Jiga-Jigai

Lai Mohammed
NBC Ta Ci Aminiya Tarar Naira Miliyan 5 Saboda Bidiyon Tona Asirin Yan Bindiga. Hoto: @thecableng.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NBC, cikin wasikar da ta aike wa kamfanin mai kwanan watan ranar 3 ga watan Agustan 2022, mai dauke da sa hannun shugabanta, Balarabe Shehu Illela, ta ce an saka tarar ne kan Trust TV saboda wallafa bidiyon wanda ya saba da dokokin NBC.

Martanin Media Trust TV

A cikin sanarwar da ta fitar, mahukunta a ta Media Trust ta ce:

"A halin yanzu muna nazarin matakin da hukumar ta dauka da abin da za mu yi, muna son mu bayyana cewa a matsayin mu na gidan talabijin, mun yi imanin cewa abin da muka yi don amfanin al'umma ne don karin haske kan matsalar yan bindiga da yadda ya ke shafan kasar mu."
“Bidiyon ya nuna tushen rigingimu tsakanin mutane da kuma matsaloli da suka haifar da rikicin makamai da ya zama tubali kan matsalar mutane na jin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

“Har ila yau, ta tattara muryoyin kwararru da manyan masu ruwa da tsaki don samar da mafita, ciki har da na Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, Sanata Saidu Mohammed Dansadau, wanda ya fito daga daya daga cikin yankin da suka fi fama da matsalar a Jihar Zamfara."

Sanarwar ta kara da cewa an gabatar da kwararru a cikin bidiyon kamar Farfesa Abubakar Saddique na Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria da Dr Murtala Ahmed Rufai na Jami'ar Usamanu Dan Fodio, wadanda sun dade suna nazari a kan lamarin.

Bidiyon ya kuma bayyana labarai marasa dadi daga mutanen da harin yan bindigan ya shafa.

Gwamnatin Buhari za ta sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

Tunda farko, gwamnatin Najeriya ta ce za ta sanya takunkumi ga gidajen rediyon Birtaniya (BBC) da jaridar Daily Trust, mai wallafa sashen Hausa na Aminiya kan shirin da suka tattara kan ta’addanci da barnar ‘yan bindiga a Najeriya a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Tana Tara Kudi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

Lai Mohammad, ministan yada labarai da al'adu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, The Cable ta ruwaito.

A kwanan nan ne wasu fafa-fayan bidiyo suka yadu a kafafen sada zumunta, inda ake nuna wakilan BBC da na Aminiya suna hira da 'yan ta'adda a cikin dazukan da suke fake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel