Jihar Ogun: Jami'a a NYSC ta caccaki 'yar bautar kasa saboda sanya zungureren siket

Jihar Ogun: Jami'a a NYSC ta caccaki 'yar bautar kasa saboda sanya zungureren siket

  • Wata 'yar bautar kasa a jihar Ogun ta harzuka wata jami'a a sansanin bautar kasa bayan da ta fito sanye da dogon siket
  • A cikin wani faifan bidiyo, jami’ar sansanin tacaccaki 'yar bautan kasar kan sanya irin wannan kayan kuma ya nemi ta bar sansanin
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun fadi ra'ayoyinsu inda akasarin mutanen suka soki abin da 'yar bautar kasan ta yi

Jihar Ogun - Wata 'yar bautar kasa da ke hidima a jihar Ogun ta gamu da matsala bayan da ta sanya zungureren siket zuwa sansanin wayar da kai na 'yan bautar kasa.

Zugureren siket da dogon hijabi ta saka amma hakan bai yiwa wata jami'a a sansanin dadi ba ganin hakan ya yi wani banbarakwai.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Wata Karamar Yarinya Tana Girgijewa Ya Burge Mutane

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawoa intante, an ga jami’ar NYSC (National Youth Serbice Corps) ta sansanin ta na yi mata fada hade da kakkausar suka kan zabar kayan da ba a saba gani a sansanin bautar kasa ba.

Sanya dogon hijabi ya jawo an caccaki wata mata a sansanin NYSC na Ogun
Ke uztaziya: Jami'a a NYSC ta caccaki 'yar bautar kasa saboda sanya zungureren siket | Hoto: @yabaleftonline
Asali: Instagram

Yayin da take sukar mata mai hijabin, jami’ar sansanin ta bukace ta da ta je ta gana da kodinetan jihar ta domin samun takardar sahhalewa daga gare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yar bautar kasan wacce a bayyane ta tsorata ta roki jami’ar sansanin da ta tausaya mata amma rokon nata bai ga nasara ba. Kafar tsegumi ta @yabaleftonline ne ta yada bidiyon a shafin Instagram.

'Yan Najeriya sun mayar da martani game da bidiyon

Mayorjnr_ ya ce:

"Kin sa zungureren siket kin hada da dogon hijab, meke damunki anti shin wurin NYSC akwai aljanu ne."

Kara karanta wannan

Bayyanar bidiyo da hotuna motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali

Kemz_kemzy ya ce:

"Tace ki bace mata da gani dai ko."

Official_jimcally ya ce:

"Ba wannan ne zai mai da ke tsarkakakka ba kanwata."

Alexis_euro_ ya ce:

"Mama babu sanki a lamarin."

Dizzkidofficial ya ce:

"Siri kunna min -Dj spinal /Asake- pallazo. siket din ne bani dariya ma."

_halal_space ya ce:

"Amma inaga wannan ya faru a can baya ko..."

Coachayere ya ce:

"Duk wannan ba komai ne a aljanna ."

Euphemiachizzy ya ce:

"Sirt din ma ni dariya ya bani"

Sabjoz ne ya ce:

"Tunda dogon hijabi take sanye dashi ba matsala don ta saka wando."

Chioma___official ya ce:

"Idan ba za ku iya bin dokar ba to kada ku yi hidimar kasa."

Matashi mai shekaru 18 ya ba da labarin yadda ya kera mota daga tarkacen karfe

A wani labarin, wani matashi dan kasar Ghana, Obed Obeng Danso na cibiyar bunkasa al'umma da fasaha ta CONVOTECH da ke garin Tarkwa a yankin yammacin kasar ya kera motarsa ta farko.

Kara karanta wannan

Mace Mai Kamar Maza: An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

Motar ta matashi mai shekaru 18 tana tafiya ne ta hanyar amfani da man fetur ba tare da wani kalubale ba yayin da aka ga tana tafiya ba tare da wani cikas ba a kan titi.

Danso ya shaidawa Ghanaweb cewa a koda yaushe yana mafarkin kera abin hawa, kuma ta hanyar azamar da ya yi, a karshe dai ya tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel