Bidiyoyin Wata Karamar Yarinya Tana Girgijewa Ya Burge Mutane

Bidiyoyin Wata Karamar Yarinya Tana Girgijewa Ya Burge Mutane

  • An gano wata kyakkyawar yarinya tana girgijewa tare da rera wakar 'buga', inda ta burge mutane da dama
  • Yarinyar tana da tsananin wayo sannan tana tafiyar da abubuwarta kamar wata cikakkiyar budurwa
  • Jama'a sun kayatu matuka da kallon bidiyoyin nata, yayinda da dama suka yi mata addu'a kan Allah ya raya ta

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wata kyakkyawar yarinya karama tana rawa.

A daya daga cikin bidiyoyin wanda shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram an gano yarinyar tana girgejewa tare da bin wata wakar turanci mai taken ‘Buga’.

Afreen
Bidiyoyin Wata Karamar Yarinya Tana Girgijewa Ya Burge Mutane Hoto: hausaa_fulanii
Asali: UGC

Yanayin yarinyar da ke abubuwanta cike da wayo kamar ba yar shekarunta ba shi yafi daukar hankalin mutane.

Ta yi shigar manyan mata dinkin Atampa doguwar riga kanta daure da kallabi sannan tsintsiyar hannunta sanye da agogon hannu.

Kara karanta wannan

An gano sabon na'uin sauro mai yada cutar maleriya a arewacin Najeriya, Cibiyar Bincike

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyoyin yarinyar a kasa:

Martanin jama’a

ubmeerat_treats ta yi martani

"lukutayen yara dai su a farin jini masha Allah, tana rera nata sumfurin wakar abunta harda jefa kafa."

fulani_maryaam ta ce:

"Kun tabbata wannan ba babban mace bace? Irin bata yi kama da karamar yarinya ba sai babban mace."

eat_with_khabs ta rubuta:

"Allah ina san yarinyar nan Allah ya mata albarka ameen."

keesous__collections ta ce:

"Ta zata ana nufin a buga abune naga har da daga kafa kaman zata buga ball."

zeenamadi__ ta ce:

"@summ_hinchi hausa fulani na nemanki"

Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

A wani labarin kuma, fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce ta yiwa masoyanta albishir da cewar suna gab da fara kallonta a cikin fina-finan kasar Indiya wato Bollywood.

Kara karanta wannan

Bayyanar bidiyo da hotuna motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali

A wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram, Rahama ta bayyana cewa ta cika farin ciki bayan samun kira daga Furodusa kuma Daraktar shirin , Hamisha Daryani Ahuja cewa tana son ta fito a wani sabon fim dinta.

Hakazalika, jarumar ta kuma wallafa wani bidiyonta tana zuba yaren Indiyanci tiryan-tiryan sai kace Ba’indiyar usuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel