Matashi mai shekaru 18 ya ba da labarin yadda ya kera mota daga tarkacen karfe

Matashi mai shekaru 18 ya ba da labarin yadda ya kera mota daga tarkacen karfe

  • Wani dalibi dan kasar Ghana na cibiyar bunkasa al'umma da fasaha ta CONVOTECH ya kera motarsa ta farko
  • Obed Obeng Danso ya kera motar ne ta hanyar amfani da tarkace karafa da akasarinsu ya samo daga wata mota mai kafa uku da aka jefar
  • Dalibin da ya koyar da kansa fasahar ya bayyana yadda lamarin ya faro, gami da yadda ya ci nasarar cimma burinsa na kuruciya

Wani matashi dan kasar Ghana, Obed Obeng Danso na cibiyar bunkasa al'umma da fasaha ta CONVOTECH da ke garin Tarkwa a yankin yammacin kasar ya kera motarsa ta farko.

Motar ta matashi mai shekaru 18 tana tafiya ne ta hanyar amfani da man fetur ba tare da wani kalubale ba yayin da aka ga tana tafiya ba tare da wani cikas ba a kan titi.

Kara karanta wannan

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

Yadda matashi ya kera mota da kansa
Yaro mai shekaru 18 ya kera mota daga tarkacen karfe, ya ba da mamaki | Hoto: ghanaweb.com
Asali: UGC

Danso ya shaidawa Ghanaweb cewa a koda yaushe yana mafarkin kera abin hawa, kuma ta hanyar azamar da ya yi, a karshe dai ya tabbatar da hakan.

Ya yi aiki da iyakar abin da zai iya samu

Duk da arzikin da Danso yake da shi, ya tsoma shi a sayo gabban wata motar da aka jefar mai kafa uku, wanda aka fi sani da ‘Aboboyaa’ a harshen Ghana, don kammala aikinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalibin kanikancin motoci ya kuma ce ya koya wa kansa da kansa yadda ake kera moto ne, inda ya samu kwarin gwiwa da ilimi daga yadda motoci masu kafa uku ke aiki.

Bayan kera motarsa ta farko, Danso ya ce yana son ya zama kwararre domin horar da wasu sana'ar ta kira; musamman matasa.

Kalli bidiyonsa:

Kin fi karfi na: Miji ya fece ya bar matarsa saboda ta haifa masa tagwaye sau biyar

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da aka garkame makarantar sakandare saboda tsoron harin 'yan bindiga

A wani labarin, tarin 'ya'ya dai albarka ce kuma abu mai kyau, amma sa'ad da aka samu tasgaro, zai iya haifar da hargitsi.

Wata mata da ta haifi tagwaye har sau biyar ta ba da labarinta mai radadin gaske na yadda tarin albarkar 'ya'ya ya zame mata nauyi.

Nalongo Gloria daga Uganda ta ce mijinta Ssalongo ya watsar da kashinta ne saboda ta ci gaba da haifa masa tagwaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel