Mutane Sun Yi Zaton 'Asirin Kudi' Na Ke Yi Saboda Irin Motar Da Na Ke Hawa, Sanatan Najeriya

Mutane Sun Yi Zaton 'Asirin Kudi' Na Ke Yi Saboda Irin Motar Da Na Ke Hawa, Sanatan Najeriya

  • Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce akwai lokacin da wasu mutane ke yada jita-jitar cewa yana 'asirin kudi' saboda zukekiyar motar da ya ke hawa
  • Tsohon gwamnan na Abia ya ce shi tun farko dama mai arziki ne don a 1982, irin motar da ya ke hawa, shi da shugaban kasa Shehu Shagari kawai ke da irinta
  • Kalu ya bayyana cewa shi ba domin samun kudi ya shiga siyasa ba domin yana ma amfani da kudin aljihunsa ya yi wa mutanen yankinsa aiki kuma bai siya gida ba tun bayan zama sanata

Sanata Orji Kalu, bulaliyar majalisar dattawar Najeriya ya ce wasu yan Najeriya na yada jita-jitan cewa 'asirin kudi' ya ke yi saboda motar da ya ke hawa

Kara karanta wannan

Daukar Dala Babu Gammo: Yadda Dan Najeriya Ya Ajiye Aikin Da Ake Biyansa Miliyan N24, Ya Koma Turai Yin Digirgir

Kalu, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce a shekarun 1982 motar da ya ke hawa shi da shugaban kasa Shagari kadai suke da irinta.

Sanata Orji Kalu a gidansa na Landan.
Mutane Sun Yi Zaton 'Asirin Kudi' Na Ke Yi Saboda Irin Motar Da Na Ke Hawa, Sanatan Najeriya. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu.
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Jihar Abia ya ce ba gaskiya bane cewa saboda kudi ya shiga siyasa domin a cewarsa yana kashe kudin aljihunsa don yi wa mutanen yankinsa hidima

Bulaliyar Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce wasu yan Najeriya sun yi zaton 'yankan kai' ya ke yi saboda zukekiyar mota mai tsada da ya ke hawa a 1982.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mr Kalu, cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook, ranar Asabar, ya ce motar ita ce 'sabuwar' Marsandi. Bai bada karin bayani game da motar ba.

"Shugaban kasa a wannan lokacin Shehu Shagari shi kadai ke amfani da irin wannan motar a lokacin," in ji shi.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

"Zan iya tunawa duk lokacin da na fitar da motar, wasu za su rika kallo na suna sha'awa yayin da wasu tsiraru suna yadda jita-jita cewa yankan kai yi."

Mr Kalu ya ce yan Najeriya su dena sauraron 'masu nufin yi masa sharri' na cewa kudi ta sa ya shiga siyasa.

"Idan har kudi ne kamar yadda ake yadawa, ai dama ina da duk abin da na ke bukata," in ji sanatan.
"Lokacin da na ke gwamna, ban taba siyan sabon gida ba. Na rasa kudi ne ma bayan shiga siyasa. Na karbi mulki ne daga shugaba na soja kuma wanda suka san Abia kafin 1999 za su fahimci irin aikin da muka yi kafin barin gwamnati a 2007.
"A yanzu, zan iya murabus a matsayin sanata domin ina kashe kudi na don yi wa mutane na hidima."

Sanatan ya koka kan cewa Najeriya kasa ce inda aka girmama mutanen da ba su yi komai ba illa rike mukami yayin da wadanda suka yi aiki tukuru suka samu arziki suna samar da ayyuka kuma ake zaginsu.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce duk abubuwan da ya aikata da ya kuma samu bisa tsautsayi ne amma banda noma, rahoton PM News.

Tsohon shugaban na mulkin soja, wanda aka zaba a karkashin mulkin farar hula a 1999, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, a wani shirin rediyo na kai tsaye tare da Segun Odegbami a Eagles 7 Sports 103.7 FM, Abeokuta.

Obasanjo ya bayyana cewa tuntuni yana alfahari da kasancewarsa manomi, rahoton The Punch ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel