Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a

Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a

  • Wasu ma'aurata biyu a Kaduna, Halima Ahmad da Suleiman Atiku sun garzaya kotun shari'a kan batun neman saki
  • Alkalin kotu ya umurci Halima ta mayarwa Atiku katifa wanda a bangarensa ya ce mallakar tsohuwar matarsa ne
  • Kotun ta umurci Aliyu ya bawa Halima N20,000 ta siya sabon katifa da N80,000 don biyan bashin da ake binta sannan ya dage cigaba da shari'ar

Kaduna - Wata kotun shari'a a Kaduna, a ranar Litinin ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad ta mayar da katifa ga mijinta da suka kwance alaka, Suleiman Atiku.

Mr Atiku, ma'aikacin hukumar gyaran hali, tunda farko ya bukaci a dawo masa da katifansa, kafin ya amince da bukatar sakinta, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararriyar jarumar Fim a Najeriya ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu tun kafin zuwa Asibiti

Gudumar alkalin kotu.
Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Halima, wacce ke zaune a Badarawa, Kaduna, a watan Afrilun 2022, ta garzaya kotun shari'a da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna ta nemi a raba ta da mijinta.

Alkali ya umurci a bawa Halima kudi ta siya sabon katifa

A yayin yanke hukuncin, alkalin ya umurci Atiku ya bawa Halima N20,000 domin ta siya sabon katifa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin kuma ya umurci Atiku ya biya Halima N80,000 domin ta biya bashin da ta ci a lokacin da suke tare a matsayin mata da miji.

Ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan bukatar neman sakin.

Tunda farko, wacce aka yi karar ta shaida wa kotu cewa a shirye ta ke ta mayar da sadakin da aka biya yayin aurenta.

Atiku ya shaida wa kotu cewa katifar ta matarsa na farko ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umurci A Yi Wa Alkalai Karin Albashi a Najeriya

Sautin Murya: Wata Da Aka Ce Matar Jarumin Fina-Finan Najeriya Ne Ta Masa Fallasa Game Da Yayansa

A wani rahoton, kun ji cewa labaru marasa dadi ne aka rika dangatawa da Jarumin Nollywood Yekini Higher wanda ake kira Itele.

Jarumin wanda ya sha suka a dandalin sada zumunta a kwanakin baya saboda cin amanar matarsa da wata jaruma, Debankee, ya hadu da fushin matarsa ta biyu saboda rashin kula da yaransu.

Matar, wacce aka ce itace matarsa ta biyu ta tuntubi shafin Gistlover inda ta yi wa jarumin fallasa.

Ta bayyana cewa yaransu suna zaune a gida tun makon da ya gabata saboda rashin biyan kudin makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel