Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umurci A Yi Wa Alkalai Karin Albashi a Najeriya

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umurci A Yi Wa Alkalai Karin Albashi a Najeriya

  • Kotun Ma'aikata Ta Najeriya ta umurci Hukumar Tatattarawa da Rarraba Kudin Shigar Gwamnati (RMAFC) ta yi wa ma'aikatan shari'a karin albashi
  • Hakan na zuwa ne bayan karar da babban lauya, Sebastian Hon mai mukamin SAN ya shigar na korafin cewa kimanin shekaru 14 kenan ba a yi wa ma'aikatan shari'ar karin albashi ba kuma darajar naira da tattalin arziki sun lalace
  • Tunda farko, Majalisar Tarayyar Najeriya da Kwamitin Kolin Shari'a na kasa sunyi kokarin sulhu a wajen kotu game da karar amma hakarsu bata cimma ruwa ba

Mai shari'a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae na kotun ma'aikata da ke Abuja ya umurci Hukumar Tatattarawa da Rarraba Kudin Shigar Gwamnati (RMAFC) nan take ta fara aiki don yi wa alkalai da wasu ma'aikatan kotu karin albashi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Kotu yanke wa jarumin Nollywood hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari

Alkalin ya yanke wannan hukuncin ne a karar da wani babban lauyan Najeriya mai mukamin SAN, Sebastian Hon ya shigar. Babban lauyan ya tafi kotun ne don neman a yi wa alkalan Najeriya karin albashi, rahoton Channels TV.

Gudumar Kotu.
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umurci A Yi Wa Alkalai Karin Albashi a Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncinsa, Mai Shari'a Obaseki-Osaghae ya bada umurnin a rika yi wa ma'aikatan kotun karin albashi a kalla duk shekara daya ko biyu idan an dauki lokaci.

Ya kuma bada umurnin a biya wanda ya shigar da karar Naira 500,000, a matsayin kudin shigar da kara da shari'ar.

Kotun ta ce akwai wadatattun hujjoji da ke nuna cewa albashin alkalai da masu shari'ar, wanda tun shekarar 2008 ne aka yi kari, bai dace da halin da ake ciki yanzu ba, saboda karyewar darajar naira, canjin kudi, da tabarbarewar tattalin arziki a kasa.

Rabon Ma'aikatan Shari'ar da karin albashi tun shekarar 2008, in ji Sebastian

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar cin mutuncin Buhari a Kogi

Alkali Obaseki-Osaghae ya kuma ce wanda aka yi karar na farko (RMAFC) ta gaza yin amfani da ikon da doka ta bada don yi wa ma'aikatan shari'ar karin albashi, tsawon shekaru 14.

Kotun ta ce akwai wasa da aiki, sakaci ta rashin son yin aiki daga bangaren RMAFC tun shekarar 2008.

Ta ce sakacin ya jefa ma'aikatan shari'ar cikin talauci da kunyatta, ta ce lamarin abin kunya ce ga kasa.

Kafin yanke hukunci kan lamarin, Mai shari'a Obaseki-Osaghe ta yanke hukunci kan batun hallarcin sauraron karar, tana mai cewa wanda ya yi karar ya gabatar da gamsassun huja don haka kotun na da hurumin sauraron karar.

Majalisa ta nemi yin sulhu amma hakan bai yi wu ba

An cigaba da sauraron karar a kotun bayan yunkurin da Majalisar Tarayya da Majalisar Kolin Alkalai suka yi a baya na yin sulhu a wajen kotu.

Ranar Ma'aikata: Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi zuwa N40,000

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

A bangare guda, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa daga N30,000 da gwamnatin tarayya ta ƙayyade zuwa N40,000.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana wannan ƙarin ne yayin taya ma'aikata murnar 'Ranar ma'aikata ta duniya' ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel