Sautin Murya: Wata Da Aka Ce Matar Jarumin Fina-Finan Najeriya Ne Ta Masa Fallasa Game Da Yayansa

Sautin Murya: Wata Da Aka Ce Matar Jarumin Fina-Finan Najeriya Ne Ta Masa Fallasa Game Da Yayansa

  • Wata da ta yi ikirarin ita ce matar jarumin Nollywood Yekini Higher wanda aka fi sani da Itele ta masa fallasa
  • A cikin wani sakon murya da ta fitar ta yi ikirarin jarumin ya yi watsi da nauyin da ke kan matarsa ta biyu da yayansa na abinci da kudin makaranta
  • A cewarta, yayansa sun shafe kwanaki a gida ba su zuwa makaranta har rufe su ta ke a gida saboda kunya amma yana da yan mata da yawa a waje

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A wannan makon, labaru marasa dadi ne aka rika dangatawa da Jarumin Nollywood Yekini Higher wanda ake kira Itele.

Jarumin wanda ya sha suka a dandalin sada zumunta a kwanakin baya saboda cin amanar matarsa da wata jaruma, Debankee, ya hadu da fushin matarsa ta biyu saboda rashin kula da yaransu.

Kara karanta wannan

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

Yekini Itele
Sautin Murya: Wata Da Aka Ce Matar Jarumin Fina-Finan Najeriya Ne Ta Masa Fallasa Game Da Yayansa
Asali: Twitter

Matar, wacce aka ce itace matarsa ta biyu ta tuntubi shafin Gistlover inda ta yi wa jarumin fallasa.

Ta bayyana cewa yaransu suna zaune a gida tun makon da ya gabata saboda rashin biyan kudin makaranta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matar ta bayyana cewa ta rufe su a gida kafin ta fita saboda kada su fita su rika gararamba a titi.

Wani sashi na sakon muryar ya ce:

"Yaran Itele suna gida tun makon da ta gabata saboda bata da kudin abinci da na makaranta, yau Litinin ta rufe su a gida saboda kunyar a gansu suna gararamba a gari ba tare da zuwa makaranta ba, ta kuma kara da cewa ba bin maza ta tafi yi a Dubai ba, aikin gida ta yi wa Oman."
"Na san cewa idan na bukaci GLB Nation su yi wa yaran karo-karo yanzu, za mu tara fiye da miliyan, amma ba zan yi hakan ba, a karon farko ba za mu taimaka ba."

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, Mijinta ya fahimci ta ci amanarsa da mutane 9 a boye

Ta ce Itele ya wuce shekaru 40 don haka abin kunya ne ya gaza kulawa da iyalansa amma yana da wasu yan matan a waje.

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin daban, shaharren mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

A cikin faifan bidiyon, Shugaban kamfanin Hypertek Digital ya yi magana ne cikin harshen Pidgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel