Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jihar Bauchi

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jihar Bauchi

  • Jami'an tsaro sun kewaye zauren majalisar dokokin jihar Bauchi bayan wani yunkuri na ƙona wurin bai ci nasara ba
  • Wannan na zuwa ne bayan rikici ya ɓarke a majalisar, inda mambobi 22 suka bukaci kakaki ya yi murabus ko su tsige shi
  • Fadar gwamnatin jihar Bauchi ta ce an ɗauki matakin ne don kare yuwuwar karya doka da oda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Yunkurin mafi rinjayen mambobin majalisar dokokin Bauchi na tsige kakaki, Abubakar Suleiman, ya gamu da cikas ranar Litinin yayin da jami'an tsaro suka kwace iko da zauren majalisar.

Punch ta ruwaito cewa rikicin da ya balle a majalisar kan shugabanci ya ɗauki sabon salo bayan wasu bara gurbi sun yi yunƙurin kone zauren majalisar.

Majalisar dokokin Bauchi.
Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jihar Bauchi Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A makon da ya gabata, mambobi 22 suka yi barazanar tsige kakakin majalisa da duk wani mai rike da muƙami idan ba su yi murabus ba bayan kaɗa kuri'ar rashin kwarin guiwa kan jagorancin su.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Leadership ta gano cewa wasu mutane da ba'a san ko suwaye ba, waɗan da ake zargin masu tada wuta ne, sun yi kokarin taɓa wani sashin ginin majalisar, amma tun kafin wutar ta je ko ina jami'an kashe gobara suka daƙile ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa jami'an tsaro suka kewaye majalisar?

Mai taimaka wa gwamnan Bauchi kan harkokin majalisa, Sani Mohammed Burra, a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Litinin, ya ce jami'ai sun kewaye majalisar ne don dakile yuwuwar karya doka da oda bayan abinda ya faru a daren Lahadi.

Honorabul Burra ya ce:

"Muna mai sanar muku cewa wasu mutane bara gurbi da ba'a san su ba sun yi yunkurin ƙona zauren majalisa da daren jiya. Sakamakon haka dakarun tsaro suka kewaye wurin domin kare yuwuwar karya doka da oda."

Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ƙi cewa komai game da lamarin.

Kara karanta wannan

Danbarwa ta ɓarke a majalisar dokokin jiha a arewa, mambobi 22 sun ɓalle, sun nemi kakaki ya yi murabus

A wani labarin kuma Wasu mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari Monguno sun kwashi kashin su a hannun Sojoji

Sojojin haɗin guiwa na kasa da ƙasa MNJTF na runduna ta uku sun yi nasarar daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Borno.

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce an kwashe fiye da a wa ɗaya ana ɗauki ba daɗi da yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel