Dakarun soji sun daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Monguno

Dakarun soji sun daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Monguno

  • Sojojin haɗin guiwa na kasa da ƙasa MNJTF na runduna ta uku sun yi nasarar daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Borno
  • Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce an kwashe fiye da awa ɗaya ana ɗauki ba daɗi da yan ta'addan
  • Wata majiya ta ce harin ka iya yuwuwa na ɗaukar fansa bayan sojojin sun sheke mayaƙan kungiyar a wasu kauyuka biyu

Borno - Dakarun sojin haɗin guiwa na ƙasa da kasa (MNJTF) sun daƙile harin ƙungiyar ISWAP a garin Monguno, jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Daily Trust ta tattaro cewa mayaƙan ISWAP, waɗan da suka zo da shiri a kan motocin yaƙi da Babura, sun kai samame garin tare da muggan makamai da karfe 1:30 na daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matar shugaban ma'aikata da aka sace ta haihu a sansanin 'yan bindiga, ta kira shi a waya

Dakarun soji.
Dakarun soji sun daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Monguno Hoto: leadership.ng
Asali: Depositphotos

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce an kwashe sama da awa ɗaya ana musayar wuta kafin daga bisani sojojin su yi nasarar tilasta wa maharan tsere wa.

Duk da babu cikakken bayani kan adadin waɗan da aka rasa, wata majiya ta ce da yuwuwar harin na ramuwar gayya ne ga kashe dandazon mayaƙan ISWAP yayin wani samame da MNJTF ta kai Sabon Tumbum da Jibularam, ƙaramar hukumar Marte.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

Majiyar ta bayyana cewa a ranar 1 ga watan Yuli, da ƙarfe 10 na dare, manyan jagororin ISWAP a cikin motocin Hilux sama da 15 suka je Sabon Tumbu daga yankin hanyar Kwalaram domin kwashe matattu da raunatattun mayaƙansu.

Majiyar ta ce:

"Sun kai matattun su zuwa yankin hanyar da ke tsakanin Kekeno da Barwati a ƙaramar hukumar Kukawa, anan aka birne su. Daga baya yan ta'adda suka tattara mayaƙan su a Jeji kafin kaddamar da hari a garin Monguno."

Kara karanta wannan

Hajji 2022: Wani Alhaji ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a jaka a Madinah

A ranar 18 ga watan Yuni, mayaƙan ISWAP suka kai hari garin Monguno, inda suka halaka Civilian Joint Task Force (CJTF) guda uku, kuma suka sace masu aikin jin ƙai uku.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sako ma'aikatan da suka sace a Zamfara, sun maida kuɗin da aka kai musu na fansa

'Yan bindigan da suka yi garkuwa da ma'aikatan lafiya a jihar Zamfara ranar Asabar da ta gabata a kan babbar hanyar Gusau-Ɗansadau, sun sako su baki ɗaya.

'Yan fashin dajin, waɗan da sunan su ya fi shahara da ƴan bindiga a Zamfara da sauran jihohin arewa ta yamma da suka hana zaman lafiya, sun kuma maida miliyan N5m da aka biya su da sunan kuɗin fansar mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel