Hukuncin namijin da yaci amanar matarsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya

Hukuncin namijin da yaci amanar matarsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya

  • Tsohon kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Aliyu Giwa, ya bayyana yadda za a iya daure mai aure shekaru 2 a gidan yari saboda zina
  • Fitaccen 'dan sandan ya sanar da cewa, za a iya daure mace ko namji mai aure da ya ci amanar abokin rayuwarsa ko kuma tara, ko duka biyun
  • Ya sanar da cewa, laifi ne da yayi karantsaye ga dokokin Penal Code dake sashi na 387 da 388 a Najeriya

Tsohon kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Aliyu Giwa ya ja kunnen 'yan Najeriya kan su tsaya da gaskiyarsu ko kuma su sha daurin shekaru biyu idan aka kama su suna cin amana.

A wata wallafar Twitter a ranar Lahadi, Giwa yace neman mata laifi ne da ke iya janyo hukuncin shekaru biyu a gidan yari.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

"Zina ga me aure laifi ne da zai iya janyo kwashe shekaru 2 a gidan kurkuku," yace.
Gudumar kotu
Ko ka/kin san zaka/ki iya yin shekaru 2 a gidan yari a shari'ance kan cin amanar mata/miji?. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Kamar yadda yace, laifin ya ci karo da sashi na 387 da 388 na dokokin Penal Code.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin bayyana dokar, ya rubuta, "Duk wanda, mace ko namiji ya taka dokar gargajiya wacce ta hana neman mata wacce laifi ce mai zaman kanta, ya sadu da wani wanda ba matarsa ba ko miji, wannan saduwar kuma ba laifin fyade bace, za a kama shi da laifin zina kuma za a hukunta shi ta hanyar yanke masa hukuncin zaman gidan yari ko a ci tarar shi ko kuma duka biyun."

Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Bilkisu Muhammad a ranar Litinin ta yi kira ga wata kotun shari'a a Kaduna da kada ta tsinke igiyar aurensu da Sirajo Mansur saboda tana son mijinta ya sauke nauyinta da ke kan shi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

Muhammad ya shigar da karar a ranar 23 ga watan Mayu, inda ya ce ya tafi Legas neman aiki amma ya kasa samar da abinci, wurin zama, tufafi da kudin makarantar 'ya'yan shi.

Vanguard ta ruwaito, ta bukaci kotu da ta sa Mansur ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makaranta.

A martaninsa, Mansur wanda ya samu wakilcin 'dan uwansa Sulaiman, ya ce wanda ake kara ya umarcesa da ya sanar da kotu cewa ta tsinke igiyar aurensu tunda matarsa ce ta maka shi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel