Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai

Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai

  • Wata matar aure mai suna Bilkisu Muhammad a ranar Litinin, ta roki alkali da kada ya tsinke aurenta da mijinta duk da ita ta kai kara
  • A cewar Bilkisu, tana son mijinta ya canza hali ne duk da baya biyan kudin haya, ciyarwa, tufatarwa da kudin makaantar 'ya'yansu
  • Wakilin Mansur da ya bayyana a gaban kotu ya ce, mijin ya bukaci alkali da ya tsinke igiyar aurensu tunda ta kai shi kotu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wata matar aure mai suna Bilkisu Muhammad a ranar Litinin ta yi kira ga wata kotun shari'a a Kaduna da kada ta tsinke igiyar aurensu da Sirajo Mansur saboda tana son mijinta ya sauke nauyinta da ke kan shi.

Muhammad ya shigar da karar a ranar 23 ga watan Mayu, inda ya ce ya tafi Legas neman aiki amma ya kasa samar da abinci, wurin zama, tufafi da kudin makarantar 'ya'yan shi.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai
Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: Facebook

Vanguard ta ruwaito, ta bukaci kotu da ta sa Mansur ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makaranta.

A martaninsa, Mansur wanda ya samu wakilcin 'dan uwansa Sulaiman, ya ce wanda ake kara ya umarcesa da ya sanar da kotu cewa ta tsinke igiyar aurensu tunda matarsa ce ta maka shi a gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa, ya yi kokarin biyan kudin haya amma mai gidan ya ki karbar kudin saboda ya riga ya bai wa wani dakin.

"A bangaren kudin makaranta, a halin yanzu yara suna rubuta jarabawa ne. Zan biya kudin makaranta bayan an kammala jarabawa," yace.

Alkali Malam Rilwani Kyaudai, ya umarci wanda ake kara da ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makarantar yaran shi.

Ya umarci mai gidan hayan da ya hallara a gaban kotu bayan ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji

Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka matar basarake, sun sace 'yan biki

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka matar wani basarake gami da raunata mutane da dama a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwoto a harin da suka kai a tsakar ranar Asabar.

An samu labarin yadda suka yi awon gaba da mutane hamsin da bakwai daga kauyuka biyu - Gebe da Alkammu. 50 daga Gebe yayin da suka yi garkuwa da bakwai daga Alkammu.

Premium Times ta tattaro yadda 'yan bindigan suka halaka matar sarkin kauyen Gebe bayan sun shiga gidan biki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel