'Yan Sanda: Ƙarawa Dogaran Osinbajo da Aisha Buhari Girma ya Tada ƙura

'Yan Sanda: Ƙarawa Dogaran Osinbajo da Aisha Buhari Girma ya Tada ƙura

  • Jami'an 'yan sanda sun matukar hassala yayin da aka karawa dogarin Yemi Osinbajo da na Aisha Buhari matsayi zuwa mataimakan kwamishinonin 'yan sandan
  • Dogaran 2 sun fara aikin 'yan sandan a 2002 daga matakin sifeta da kwalin sakandare yayin da wadanda suka fara aikin daga matakin ASP a shekara daya dasu har yanzu suke CSP
  • Mutane da dama na ganin hakan a matsayin rashin adalci duba da yadda ya kamata a dinga karin girma duk bayan shekaru hudu ko uku, inda jama'a suka siffanta hakan da fifita wasu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ana cigaba da cece-kuce cikin 'yan sandan Najeriya bayan karin girman da aka yi wa Ayoola Oladunni da Usman Shugaba, dogaran mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matar Shugaban kasa Aisha Buhari ba bisa ka'ida ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda tare da amincewar Sifeta-janar Usman Alkali Baba, cikin kwanakin nan aka karawa duka dogaran biyu Oladunni da Shugaba girma zuwa mataimakan kwamishinan 'yan sandan (ACP) daga mukamansu na baya CSPs.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

ADC Usman Shugaba
'Yan Sanda: Ƙarawa Dogaran Osinbajo da Aisha Buhari Girma ya Tada ƙura. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike da Daily Trust tayi ya nuna yadda biyun, wadanda suka fara aikinsu a 2002 a matsayin Cadet Inspectors bayan shigowa harkar aikin 'yan sanda da takardun sakandaren su, yayin da abokan aikinsu da suka fara aikin 'yan sanda da kwalin kwalejinsu na digirin farko a lokaci daya dasu har yanzu suna matakin CSPs.

Bayan cigaba da bincike an gano yadda abokan aikin dogaran biyu da suka kammala digiri kafin fara aikin 'yan sanda a 2002 sannan sun fara ne daga matakin ASPs.

Hakan na nuna an musu karin girma sau uku yayin da aka wa biyun karin girma sau biyar.

A yadda ya kamata, jami'in da ya shigo aikin 'dan sanda a matsayin Cadet Inspector ana masa karin girma so biyar kafin ya kai matakin mataimakin kwamishinan 'yan sandan (ACP); daga ASP zuwa DSP; SP; zuwa CSP kafin ya kai matakin ACP.

Kara karanta wannan

Sarkin Minna ya shiga tsakanin rikicin yan sanda da yan banga

Ta daya bangaren, jami'in da ya fara aikin 'yan sandan a matakin Cadet ASP na samun karin girman matakai uku kafin ya kai matakin CSP. Hakan yana nuna daga ASP zuwa DSP zuwa SP zuwa CSP.

Yayin da wasu jami'an tsaron da suka zanta da Daily Trust a daren jiya, sun bayyana yadda ake karin girma duk bayan shekaru hudu, wasu sun ce ana yi bayan shekaru uku, sai dai an gano ana karin girman ne bayan duba da kokarin mutum da sauran abubuwa.

Sai dai kuma, karin girman da aka yi kwanan nan ya fusata wasu jami'an 'yan sandan wanda ya janyo takaici, inda wasu jama'an suke fuffukan an fifita wadanda ake so a kan "wanda suka cancanta da bin hanyar da ta dace" ba kawai zai dankwafar da karfin guiwar ba, sai dai ma ya zama hatsari ga tsarin 'yan sandan kasar.

Wani daga cikin fusatatun jami'in 'yan sandan da Daily Trust ta zanta dashi tare da bukatar a sakaya sunansa saboda tsaro ya ce,

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

"Na daga cikin dalilan da yasa bangarori da dama na kasar nan suke ci baya shi ne aukuwar irin wannan lamarin, inda ba a bin matakan da suka dace.
"Ba dole hakan ya zama matsala a yanzu ba sai nan gaba idan maganar karin girma yazo, za su kalli yadda suka kai matakin da suke. Idan zaku tuna wannan na daya daga cikin ikicin da akai da tsohon ADC shugaban kasa Jonathan, DIG Jitoboh, wanda ya dakatar dashi daga zama IGP. Mutane da dama suka tuhumi yadda aka yi saurin kara masa girma," a cewarsa.

Yayin jawabi kan karin girman, tsohon kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayya, Lawrence Alobi ya ce karin girma ba bisa ka'ida ba ba abu bane mai kyau da martabar jami'an tsaro.

A cewarsa, "Hakan bai kyautu ba, saboda a matsayin ka na Cadet Inspector, ya kamata a fara tabbatar da kai a matsayin Sifeta.
"A ganina, da mamaki wanda ya fara aiki a matsayin sifeta ya wuce wanda ya fara a ASP har ya zama ACP yayin da Cadet ASP yake a matakin CSP. Wannan ba adalci bane kuma hakan bai dace ba."

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

Asali: Legit.ng

Online view pixel