Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

  • Rahotanni sun bayyana yadda 'yan bindiga ke barazana ga rayukan mazauna garuruwan Arewacin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne daga jihohin Zamfara da Filato, inda tsagerun ke afkawa mazauna ba gaira ba dalili
  • A cewar majiya, an kori wasu tare da hallaka da dama daga cikin mazauna kauyukan da ke da tazara da jami'an tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Akalla al'ummomi 30 ne 'yan bindiga suka tasa a matsugunansu a yankunan jihar Zamfara a cikin wata daya, inji dan majalisar tarayya mai wakilar Gummi/Bukkuyum, Suleiman Abubakar Gumi

Jigon na siyasa ya bijiro da batun ne a yayin gabatar da wani kudiri kan bukatar kara yawan jami'an sojoji ga yankunan da abin ya shafa a jihar domin ganin karshen matsalolin da ke ta'azzara.

Yadda 'yan bindiga ke barna a Zamfara da Filato
Bayan gwamna ya ce kowa ya dauki bindiga, tsageru sun fatattaki mazauna Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar Gumi, ‘yan bindiga sun farmaka wasu al’ummomi a jihar, inda suka hallaka akalla mutane 16, tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Hakazalika, ya koka da cewa, sun yi awon gaba da shanu, tare da lalata dukiyoyi gami da kona ofisoshin ‘yan sanda da kuma kayan abinci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, mazauna yankunan na wayar gari da rikice-rikice tade tashe-tashen hankula daga tsagerun 'yan bindigan yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma nanata cewa, mazauna kauyuka kusan 71 suka daidaice, suka tsallake matsugunansu; yayin da manoma suka haure gonakinsu domin tsira da rayukansu.

Ya ce tsagerun sun kakaba haraji kan mazauna yankin, tare da talauta su da wawasar kudin fansa daga wadanda suka yi garkuwa da su.

Bangaren jihar Filato

A bangare guda kuma, ‘yan bindiga sun fitar da sabuwar sanarwar kowa ya tattara nasa-ya-nasa a kauyukan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soja, Anguwar Yuhana da Anguwan Mangu da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Mazauna yankin sun ce wasu ‘yan bindiga da ke rufe da fuska sun dura wa al’ummomin inda suka bukaci ko dai su tattara su bar yankin nan da kwanaki biyar ko kuma su fuskanci fushin ta'addanci.

Ubale Pinau, wani mazaunin garin Pinau, ya shaida wa jaridar Daily Trust a jiya cewa ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari a yankin, inda suka shawarce su da su fice idan ba haka ba su fuskanci abin da zai biyo baya.

Ya ce mutane da dama sun fara tururuwa zuwa garin Oinau mai tazarar kilo mita 11 da zagayen kauyukan, da sauran manyan garuruwa yankin domin tsira.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Ishaku Takwa, ya ce bai san da lamarin ba.

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

A wani labarin, Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta ce umarnin da ta bai wa mazauna kuma farar hula na mallakar bindigogi don kare kansu, ba wai ana nufin kowa ya mallaki bindiga ne sakaka ba.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, inji rahoton Daily Trust.

A sabon matakin da gwamnatin jihar ta dauka kan 'yan ta'adda, ta ce za ta aike da fam 500 na ba da lasisin mallakar bindiga ga masarautun jihar 19.

Asali: Legit.ng

Online view pixel