'Yan Daba Sun Jefi Alkali Da Ɗuwatsu Yayin Zaman Kotu, An Fice Da Shi Ba Shiri

'Yan Daba Sun Jefi Alkali Da Ɗuwatsu Yayin Zaman Kotu, An Fice Da Shi Ba Shiri

  • Wasu matasa sun afka kotun Jihar Bayelsa sun fattaki alkali da lauyoyi yayin da ake zaman shari'a da duwatsu da duka
  • Matasan sun kawo harin ne saboda alkalin ya dage sai ya saurari wata shari'a kan zaben shugabanin APC da aka yi a jihar a bara
  • Shugaban APC na jihar, Dr Dennis Otiotio-Odoni wanda ya nisanta mambobin APC da harin amma wani cikin wadanda aka yi wa duka ya ce yan APC suka doke shi

Bayelsa - Wasu yan daba fiye da 30 sun kawo cikas a kotu yayin da ake sauraron shari'ar taron zaben shugabannin mazabu, kananan hukumomi da Jiha ta jam'iyyar APC a babban kotun Jihar Bayelsa, Daily Trust.

Wanda ya shigar da karar, Alex Blackson da dan uwansa, Osom Blackson sun jikkata yayin turmutsi a kotun, yayin da shi kuma Alkali da ke shari'ar, Justice Nayai Aganaba, ya sha jifa da duwatsu.

Kara karanta wannan

An Yanke Wa Matar Aure Hukuncin Sharar Harabar Kotu Saboda Lakaɗa Wa Makwabciyarta Duka a Kaduna

'Yan Daba Sun Jefi Alkali Da Ɗuwatsu Yayin Zaman Kotu, An Fice Da Shi Ba Shiri
'Yan Bindiga Sun Jefi Alkali a Kotu a Bayelsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Daga bisani, dan sanda da ke tsaron alkalin ya fice da shi zuwa wani wuri don tsare lafiyarsa.

An fatattaki mafi yawancin lauyoyin, yayin da wadanda suka taho tare da mai shigar da karar su kuma aka lakada musu duka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

News Express ta rahoto cewa yan daban sun fusata ne saboda alkalin ya dage sai ya saurari karar da Alex Blackson ya shigar na neman kotun ta soke zaben da aka yi a bara.

An yi harbe-harbe a sakatariyar APC na jihar bayan yan sanda sun yi yunkurin kama wasu jiga-jigan APC kan zarginsu da hannu kan harin da aka kai kotun.

An rahoto cewa an kama mutum biyu.

Jam'iyyar APC ta nesanta kanta daga harin da aka kai kotun

Shugaban APC na jihar, Dr Dennis Otiotio-Odoni wanda ya nisanta mambobin APC da harin da aka kai a kotun, ya yi ikirarin cewa magoya bayan PDP ne suka kai harin.

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

Ya ce ya yi imanin kotu tana da ikon da za ta warware matsalolin da ke jam'iyyar ya kuma bukaci yan sanda su binciko wadanda suka kai harin.

Ya ce:

"Babu ruwan APC da harin da aka kai kotu. Mu jam'iyya ne mai bin doka kuma mun yi imanin cewa kotu za ta yi adalci. Muna Allah wadai da wannan harin muna kira yan sanda su binciko wadanda suka aikata."

Lauyan wanda ya yi karar, Barista P.J. Fawei, ya bayyana harin a matsayin rashin girmama kotu.

Jigo a APC kuma dan uwan wanda ya yi karar, Osom Blackson ya shaida wa manema labarai cewa wadanda suka yaga masa riga tare da dirka masa naushi sanannun yan APC ne.

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

Wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164