An Yanke Wa Matar Aure Hukuncin Sharar Harabar Kotu Saboda Lakaɗa Wa Makwabciyarta Duka a Kaduna

An Yanke Wa Matar Aure Hukuncin Sharar Harabar Kotu Saboda Lakaɗa Wa Makwabciyarta Duka a Kaduna

  • Kotun Majisatare da ke zamanta a Kaduna ta yanke wa matar aure, Hadiza Ahmed hukuncin sharar harabar kotu na kwana biyar
  • An yanke mata hukuncin ne sakamakon duka da ta yi wa makwabiyarta Farida Musa sakamakon fada da suka yi
  • Sufeta Chidi Leo, dan sanda mai shigar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashi na 173 na dokar Penal Code ta Jihar Kaduna, 2017

Kaduna - Alkalin kotun Majistare Ibrahim Emmanuel, a ranar Alhamis, ta umurci wata matar aure, Hadiza Ahmed, ta share harabar kotu na tsawon kwana biyar saboda lakada wa makwabciyarta duka.

Mr Emmanuel ya bada umurnin ne bayan Hadiza ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda

An Yanke Wa Matar Aure Hukuncin Sharar Harabar Kotu Saboda Lakaɗa Wa Makwabciyarta Duka
Matar Aura Za Ta Share Harabar Kotu Saboda Lakada Wa Makwabciyarta Duka a Kaduna. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

"An umurci ki da ki rika zuwa kotu kina share harabar kotun na tsawon kwana biyar karkashin sa idon rajistar kotun.
"Wannan hukuncin zai zama izina ga wasu da ba su son su zauna lafiya tare da makwabtansu," in ji shi.

Dan Sanda mai gabatar da kara ya magantu kan abin da ya faru

Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Chidi Leo ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Maris a Tundun Wada Kaduna.

News Digest ta rahoto cewa Leo ya ce Hadiza, ba tare da wani tsokana ba ta fara zagin Mrs Farida Musa, wanda hakan ya yi sanadin suka yi fada.

Ya kara da cewa yayin fadan, wanda aka yi karar ta a kotun ta lakada wa wanda ta shigar da karar duka.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

Laifin, ya ce ya saba wa sashi na 173 na dokar Penal Code ta Jihar Kaduna, 2017.

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel