Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya saka labule tare da yan kungiyar tsoffin ministocin gwamnatin PDP
  • Gwamnan ya zargi gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Buhari da lalata kasar tare da kawo rabuwar kai sosai a tsakanin al’umma
  • Mai son zama shugaban kasar a zaben 2023, ya sha alwashin aiki tare da kowa ba tare da la’akari da kabilanci ko san zuciya ba idan har ya yi nasara a zabe

Abuja - Gwamnan jihar Bauchi kuma mai aniyar son zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bala Mohammed ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake magana a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, a wajen wani taro da tsoffin ministocin gwamnatin PDP suka shirya, Mohammed ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta lalata komai da komai na kasar, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Ya Zama Dole a Bar Kudu Maso Gabas Ta Mulki Najeriya a 2023

Mohammed ya bayyana gwamnatin Buhari a matsayin mai nuna son kai, inda ya kara da cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai gudanar da gwamnati mai yi da kowa.

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta
Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta Hoto: The Cable
Asali: UGC

Mohammed ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kasar ta tarwatse. Babu Najeriya a karkashin APC. Kasar ta rabu da yawa. Me yasa kasar nan ta rabu da yawa? Ya zama dole mu rage dacin ran da ake ciki. APC ta lalata komai. Duk son zuciya ne.
“Mu bama kabilanci a matsayinmu na yan damokradiyya. Ba za mu taba zama gwamnatin yanki ba.”

Mohammed ya ce akwai bukatar a rage yawan ciyo bashi a kasar wanda ya karu sosai a karkashin gwamnatin Buhari.

“Za ku taimaka wajen sake inganta Najeriya ta hanyar hada kai a wannan kokarin.
“Ba za mu dauki APC da wasa ba. Suna shirya nau’ikan barazana amma mun jajirce."

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Facebook, Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

A nasa bangaren, Saminu Turaki, shugaban kungiyar tsoffin ministocin PDP, ya ce Mohammed yana daya daga cikin tawagar da za su dawo da karfin jam’iyyar adawa, rahoton Daily Post.

Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse

A wani labarin kuma, Mai martaba sarkin Dutse, Nuhu Mohammadu Sanusi, ya goyi bayan takarar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.

Da yake magana a yayin da ya karbi bakuncin Amaechi a fadarsa da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, Sanusi ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai gaskiya.

Sarkin ya ce Amaechi na da dukkanin abun da kasar ke bukata daga shugaba, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel