Da dumi-dumi: Mai son gaje kujerar Buhari daga PDP ya hakura, ya barwa Peter Obi

Da dumi-dumi: Mai son gaje kujerar Buhari daga PDP ya hakura, ya barwa Peter Obi

  • Wani sabon ci gaba ya samu a jam'iyyar PDP a daidai lokacin da zaben Najeriya ke kara kusantowa nan da 2023
  • Doyin Okupe daya daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ya janye daga takarar
  • Jigon na PDP, bayan ya bayyana matakinsa na ficewa daga takarar, ya bayyana goyon bayansa ga wani dan takara, Peter Obi

Abeokuta, jihar Ogun – Dr Doyin Okupe, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP ya fice daga takarar shugaban kasa a 2023.

Okupe dai na daya daga jerin yan takarar da a baya suka nuna sha’awarsu ta neman gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jam'iyyar adawa ta PDP.

Jiga-jigai daga jam'iyyun siyasar Najeriya na ci gaba da ayyana kudurin gaje kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Dan takarar shugaban kasa ya janye
Da dumi-dumi: Mai son gaje Buhari daga PDP ya hakura, ya barwa Peter Obi | Hoto: vanguardngr.com

Daily Trust ta ruwaito cewa jigon na PDP, ya sanar da matakinsa na ficewa daga takarar a kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), Iwe Iroyin da ke Abeokuta a jihar Ogun a ranar Laraba, 30 ga Maris.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2023: Okupe ya marawa Peter Obi baya

Okupe ya ce shi da magoya bayansa za su goyi bayan takarar shugaban kasa ta tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, kuma suna nan daram sai ya samu tikitin PDP a zaben badi.

Ya kuma nemi duk sauran 'yan takarar shugaban kasa a Kudu; Cif Dele Momodu, Sanata Pius Anyim, da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, da su bayyana goyon bayansu ga takarar Obi.

Okupe ya caccaki shugabancin jam’iyyar PDP na kasa kan yadda har yanzu ta gaza wajen warware shiyyar da za ta fitar da dan takarar shugaban kasa na gaba.

Na yi abin da Afenifere suka yi, in ji Okupe

Jigon na PDP ya ce ya hada kai da kungiyar Afenifere, wata kungiyar al’adun kabilar Yarbawa, kuma ya dauki matakin janyewa ne domin a samu daidaito da adalci.

A kalamansa:

“Don daidaita kaina da muradin dattawanmu da kuma tabbatar da gaskiya da adalci, na yarda a bainar jama’a cewa tilas ne a mika wa yankin Kudu-maso-Gabas takara a 2023; wato Inyamurai."

Peter Obi dai na daga cikin mutanen yankin Kudu da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A makon jiya ne ya bayyana hakan ga ilahirin jama'a, jim kadan bayan da Atiku ya bayyana tsayawa takara a 2023 karkashin PDP.

Sanata Kwankwaso ya yi karin haske a kan ainihin dalilin da ya sa dole ya bar tafiyar PDP

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi bayanin abin da ya sa ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Jaridar Daily Trust ta ce Rabiu Musa Kwankwaso ya shaidawa manema labarai hikimarsa na yin watsi da jam’iyyar da ya nemi takarar Najeriya a 2019.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Kwankwaso ya ce kimanin watanni 11 da suka wuce aka bijiro da maganar kujerun shugabannin shiyyoyi a jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel