Kazantar da baka gani ba: Bidiyon yadda wani ke buga ruwan roba da hannu ya girgiza intanet

Kazantar da baka gani ba: Bidiyon yadda wani ke buga ruwan roba da hannu ya girgiza intanet

  • Bidiyon wani matashi da ya yi amfani da hannayensa wajen rufe bakin tarin robobin ruwa da ake son sayar wa jama'a ya harzuka jama'a a intanet
  • Mutanen da suka kalli faifan bidiyon sun ce abin takaici ne yadda rashin aikin yi ya sanya mutane da yawa suka zama 'yan kasuwan ci da karfi
  • A cikin faifan bidiyon, mutumin da aka nuna ba shi da riga kuma ba tare da safar hannu ba ya cika teburi da taron robobin ruwa

Bidiyon da ke nuna wani mutum na buga ruwan roba da hannunsa a wani yanayi na rashin tsafta duba da irin wannan aiki ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

A cikin faifan bidiyo da Yabaleft Online ya yada a Facebook, mutumin ya yi amfani da hannayensa ne wajen rufe bakin robobin ruwan a lokacin da ya jera su a kan teburi a gefensa.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon wani gidan tuwo mai ban mamaki, inda attajirai ke fakin motocinsu su kwashi girki

Yadda wani ya girgiza intanet saboda ruwan roba
Kazantar da baka gani ba: Bidiyon yadda wani ke buga ruwan roba da hannu ya girgiza intanet | Hoto: Yabaleft Online
Asali: Facebook

Ku tafasa ruwa ku sha kawai

A can nesa kuwa, an hango tarin ruwan leda a cikin dakin da yake aikin. Mutane da yawa sun yi mamakin dalilin da ya sa yake amfani da hannunsa maimakon na'urar da aka tanada saboda aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai ‘yan Najeriya da suka ce faifan bidiyon ya nuna gaskiyar lamari cewa tafasa ruwan sha ya fi sayen na leda ko na roba.

Kalli bidiyon:

A lokacin rubuta wannan rahoto, faifan bidiyon ya tattara ra'ayoyi sama da 2,000 da inda mutane kusan miliyan 1 suka kalle shi.

Wannan ai shan datti ne - martanin jama'a

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kamar haka:

Chidiebere Rex ya ce:

"Gaskiya gara ka tafasa ruwanka a zamanin nan da ka sha wannan gurbataccen ruwa da lalataccen ruwa, Allah ne kadai ne zai ceci mutum a kasar nan."

Kara karanta wannan

Matashin Miloniya Ya Baje Kolin Hadadden Gidansa da Tsadaddiyar Motar Benz, Bidiyon Ya Yadu

Emenogu Chibueze Emmanuel ya ce:

"Da hannun da injin za su yada cututtuka da sauran abubuwa masu gurɓbta ruwa a cikin ruwan idan ba a yi bi ka'idojin tsabta da kyau ba."

Fola Elizabeth Hussaini ta ce:

"Jama'a bana shan ruwan famfo, rijiyar burtsatse ko rijiya, roba kawai nake sha, don Allah ku zo ku ga wannan kuma ku taya mu shan ruwan rijiyarmu."

Peace Aimurie Odin-Okoruwa ya ce:

"Watakila injin ya lalace ne kuma me kuke tsammani a kasar da kowa ke samarwa kansa aikin yi."

Emmanuel Emilex Azubuike ya ce:

"Idan ka samu dama ka ga yadda ake hada akasarin abubuwan da mu ke ci ba za ka yarda ma ka sake cin komai ba.... Allah dai ya cece mu kawai."

Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara

A wani labarin, mazauna yankin Iyana-Isashi a Legas sun wayi gari da tashin hankali bayan wata kyakkyawar budurwa ta zama Bebiya bayan kai wa Saurayinta da suka haɗu a Facebook ziyara.

Kara karanta wannan

Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Mutum Da Ya Lika Masa Kudi a Wajen Shagalin Bikinsa, Bidiyon Ya Yadu

Vanguard ta rahoto cewa budurwan wacce ta fito daga jihar Benuwai, amma ta na zaune a Patakwal, jihar Ribas ta rasa maganarta ne bayan kwana a jikin saurayinta.

Lamarin ya soma ne daga tashi da safe, bayan Matashiyar ta tashi, ta ɗauki Ruwan Leda kuma ta fita tsakar gida domin goge bakinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel