Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara

Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara

  • Wata budurwa da ta niƙi gari tun daga Patakwal har Legas ziyartar Saurayi, ta wayi gari bata iya magana
  • Bayanai sun nuna cewa mutanen yankin sun tashi cikin tashin hankali bayan faruwar lamarin ba zato ba tsammani
  • Yan sanda sun kama wanda ake zargi, kuma ya ce ta tashi lafiya ƙalau har magana ta masa

Lagos - Mazauna yankin Iyana-Isashi a Legas sun wayi gari da tashin hankali bayan wata kyakkyawar budurwa ta zama Bebiya bayan kai wa Saurayinta da suka haɗu a Facebook ziyara.

Vanguard ta rahoto cewa budurwan wacce ta fito daga jihar Benuwai, amma ta na zaune a Patakwal, jihar Ribas ta rasa maganarta ne bayan kwana a jikin saurayinta.

Lamarin ya soma ne daga tashi da safe, bayan Matashiyar ta tashi, ta ɗauki Ruwan Leda kuma ta fita tsakar gida domin goge bakinta.

Kara karanta wannan

Badakalar kwalin NYSC: Kullun sai na yi kuka har tsawon watanni uku, Tsohuwar ministar Buhari

Taswirar jihar Legas.
Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A wannan lokacin ne ta fahimci ta zama Bebiya, ba zata iya yin magana ba, sai dai Saurayin nata yace lafiya ƙalau suka tashi.

Saurayin ya ce:

"Na haɗu da ita a kafar sada zumunta, muka kulla abokantaka kuma muka fara soyayya. Makon da ya gabata ta zo har Legas daga Patakwal domin kawo mun ziyara."
"Mun kwashe lokaci tare komai lafiya ƙalau har zuwa safiya lokacin da ta tashi, ta fita goge baki. Ta ɗauki ruwan Leda a jakar "Pure Water' a cikin gidan ta nufi waje, tana gama goge baki ta nemi bakin magana ta rasa."
"Na ji tsoro sosai saboda lokacin da ta tashi da safe sai da ta mun magana kafin ta ɗauki ruwan ta fita waje."

Wane mataki mutane suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2

Rahotanni sun bayyana cewa bayan jaraba duk wani kokari na dawo mata da magana ya ci tura, mutane sun faɗa wa yan sandan Caji Ofis ɗin Iyana-Isashi domin su kama wanda ake zargi.

Da yake tabbatar da kama mutumin kakakin yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, yace jami'ai sun kama wanda ake zargi amma daga baya suka sake shi bayan iyayen budurwar sun zo.

Iyayenta sun kafe cewa a ba su ƴarsu domin su koma da ita gida a jihar Benuwai, su nema mata magani.

"Bayan kwararan shaidu sun tabbatar da cewa iyayen budurwar ne, muka ɗamƙa musu ita a hannun su," inji Kakakin yan sanda.

A wani labarin kuma Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Wani Magidanci ya halaka matarsa ta hanyar lakaɗa mata dukan kawo wuka kan wani karamin saɓani da ya haɗa su.

Lamarin wanda ya faru a jihar Delta, ya sa Mutumin tsere wa, amma dakarun yan sanda suka nemo shi kuma suka damƙe shi.

Kara karanta wannan

Nufin Allah ne: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class'

Asali: Legit.ng

Online view pixel