Zargin cin hancin Dala 25,000: Yadda aka kaya tsakanin MD na ASD Motors da Shehu Sani a kotu

Zargin cin hancin Dala 25,000: Yadda aka kaya tsakanin MD na ASD Motors da Shehu Sani a kotu

  • Manajan Darakta na ASD Motors, Muktar Dauda, ya fito a shari'ar tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani
  • EFCC dai na tuhumar Shehu Sani da laifuffuka biyu, daga ciki akwai karbar Dala 25,000 daga hannun shugaban kamfanin ASD Motors, Alhaji Sani Dauda
  • Muktar Dauda ya yi bayani filla-filla kan haduwarsa da tsohon sanatan, amma ya ce bai san kawunsa ya ba wani kudi da sunan cin hanci ba

Wani shaidan mai kara, Muktar Dauda, ya bayar da shaida kan tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, a ranar Laraba, 23 ga watan Maris.

Gwamnatin tarayya na tuhumar Sanata Sani a kan wasu tuhume-tuhume biyu da suka hadakarbar kudi dala 25,000 daga shugaban kamfanin ASD Motors, Alhaji Sani Dauda, da nufin ba jami’an EFCC da ke bincikensa cin hanci, rahoton Independent.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Lauyan mai kara, Abba Mohammed shine ya yiwa Mista Dauda, wanda ya gabatar da kansa a matsayin Manajan Darakta na ASD Motors Ltd jagoranci.

Zargin cin hancin Dala 25,000: Yadda aka kaya tsakanin MD na ASD Motors da Shehu Sani a kotu
Zargin cin hancin Dala 25,000: Yadda aka kaya tsakanin MD na ASD Motors da Shehu Sani a kotu
Asali: Original

Saidan ya bayyana cewa ya san Sani ne saboda ya zo siyan mota a kamfaninsa ASD Motors kuma cewa ASD na nufin Alhaji Sani Dauda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shaidan ya ce:

“Na san wanda ake kara, Sanata Shehu Sani a ranar 23 ga watan Disamban 2019, da misalin karfe 8:00 na dare, ina zaune a ofishina lokacin da ya zo tare da Ciyaman dina cewa yana bukatar wata mota Peugoet 508.
“Ni da kaina na rubuta masa kiyasin kudin motar sannan ya bar ofishina ya tafi ofishin maigidana.
“Da zai wuce, ya zo ofishina inda ya bukaci asusun bankin da zai tura kudin motar, sannan na bashi asusun bankin kamfaninmu.
“Amma tun lokacin, ban sake jin doriyarsa ba.”

Kara karanta wannan

Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

Mista Muktar ya ci gaba da bayyana cewa a kamfanin ASD Motors, ana sayar da motoci ta hanyar bayar da takardar shedar da ke dauke da bayanai kuma idan mutum ya nuna sha’awarsa, sai a bayar da takardar kiyasin kudin.

Sai dai ya ce bayan basa takardar kiyasin kudin, Shehu Sani bai biya kudin a asusun ASD ba, Daily Nigerian ta rahoto.

A yayin da lauyan Shehu Sani, Abdul Ibrahim, SAN ya yi masa tambayoyi, Mista Muktar ya shaida wa kotun cewa kawunsa, Sani Dauda, shi ne shugaban kamfanin ASD Motors kuma yana cikin tsarin kamfanin.

Kan ko kawunsa ya fada masa cewa ya baiwa wani kudi a matsayin cin hanci, Muktar ya ce bai da masaniyar cewar kawunsa ya ba wani kudi a matsayin cin hanci.

A ranar 23 ga watan Janairun 2020, an bayar da belin Sani kan naira miliyan 10, bayan gurfanar da shi da EFCC ta yi kan tuhume-tuhume biyu.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje

Hukumar yaki da rashawar ta yi zargin cewa Sani ya karbi dala miliyan 25 daga shugaban kamfanin ASD, Sani Dauda, ta hanyar damfara.

Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan

A gefe guda, mun ji a baya cewa an cigaba da zaman wannan shari’a a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2020 a wani babban kotun tarayya da ke garin Abuja.

Bayan an amince da Alkalin da zai saurari karar, har an zauna an saurari hujjar da aka gabatar na wata waya tsakanin Sani da Dauda cikin harshen Hausa.

Alkali ya saurari wannan waya da aka yi na tsawon minti 20, an yi kokarin sauraron wata wayar da aka yi da harshen Ingilishi, amma abin ya faskara a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel