Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan

Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan

- Alkali ya zauna a game da shari’ar Sanata Shehu Sani da Hukumar EFCC

- EFCC ta gabatar da hujjar wata waya da Shehu Sani ya yi da Sani Dauda

- Bayan an saurari hujjoji, Alkali ya daga zama sai cikin watan Maris, 2021

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta cigaba da shari’a da tsohon Sanatan jihar Kaduna, Kwamred Shehu Sani.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an cigaba da zaman wannan shari’a a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2020 a wani babban kotun tarayya da ke garin Abuja.

Bayan an amince da Alkalin da zai saurari karar, har an zauna an saurari hujjar da aka gabatar na wata waya tsakanin Sani da Dauda cikin harshen Hausa.

Alkali ya saurari wannan waya da aka yi na tsawon minti 20, an yi kokarin sauraron wata wayar da aka yi da harshen Ingilishi, amma abin ya faskara a jiya.

KU KARANTA: Shehu Sani ya shigar da EFCC kotu ya na neman N100m

Lauyan tsohon ‘dan majalisar dattawan, A. A Ibrahim ya ce ba ya wurin a lokacin da wanda ya kai kara a kotu ya gabatar wa jami’an EFCC da wannan kudi $25,000.

A.A Ibrahim ya tabbatar da cewa wanda ake kara bai amsa laifinsa a takardun da ya sa hannu ba.

Alkali ya tambayi Lauyan ko an yi wa tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu tambaya, ganin cewa ya na cikin wadanda sunansu ya fito a korafin da aka gabatar.

Lauyan da ke kare Sanata Shehu Sani ya ce an yi hira da Magu, kuma ya karyata wadannan zargi. A karshe an dakatar da zama sai zuwa ranar 16 ga watan Maris, 2021.

KU KARANTA: A lokacin Magu, wasu sun ci karensu babu babbaka a EFCC- Sani

Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan
Sanata Shehu Sani Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Kun san cewa EFCC ta na tuhumar Shehu Sani da laifuffuka biyu, daga ciki akwai karbar fam Dala 25,000 daga hannun shugaban kamfanin ASD Motors, Alhaji Sani Dauda.

Hukumar ta ce an yi amfani da kudin ne domin a ba jami’an EFCC da ke binciken Sanatan cin hanci.

An rahoto cewa Sanata Shehu Sani ya yi ikirarin zai yi amfani da matsayinsa wajen taimaka wa Sani Dauda a kotu saboda alakarsa da Alkalin Alkalai na Najeriya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel