Miji, mata da yara biyu sun tsallake rijiya da baya yayinda fankar sama ta fado musu cikin dare

Miji, mata da yara biyu sun tsallake rijiya da baya yayinda fankar sama ta fado musu cikin dare

  • Wata mata, a shafinta na Facebook ta mika godiyarta ga Allah kan yadda ya ceci iyalanta cikin dare
  • Matar mai suna Yvonne Stanley ta bayyana cewa fanka ta fado kan gadonsu cikin dare yayinda suke kwance
  • Cike da mamaki da godiya, ta bayyana cewa babu abinda ya sameta da 'yayanta guda biyu

Wata 'yar Najeriya mai suna Yvonne Stanley ta bayyanawa ma'abota shafin Facebook yadda Allah ya ceci iyalinta cikin dare yayinda fanka ta fado musu daga sama.

A jawabin da ta daura a shafinta ranar Laraba, 23 ga Maris, ta bayyana cewa fankar ta fado musu yayinda ita da mijinta ke gab da kwanciya bacci, amma yaranta biyu sun kwanta.

A cewartsa, wannan abu ya faru ne misalin karfe 11:55 na daren Talata.

Kara karanta wannan

Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Miji, mata da yara biyu
Miji, mata da yara biyu sun tsallake rijiya da baya yayinda fanka ta fado musu cikin dare Hoto: Yvonne Stanley
Asali: Facebook

Yvonne ta yi mamakin yadda suka tsallake rijiya da baya

Yayinda take godiya ga Allah bisa wannan ceto, ta ce daidai inda ita da mijinta ke zama fankar ta fado.

Tace:

"Daren jiya misalin karfe 11:55 na dare. A gaba na da mijina wannan fankar ta fado ba tare da cewa tana da matsala ba kuma ko alamu bamu gani ba.
"Allah kadai ya san yadda yarana suka kwanta a dan lungu duk da yadda suka birgima idan suna bacci."
"Ko kadan fankar bata tabasu ba.

Ga ra'ayin wasu yan Najeriya kan lamarin

Dalha Yusuf yace:

"Shi Yasa Bana son fankar Sama"

Zainuddeen Zaid:

Nima jiya ina cire riga na daga hannu sama kawai sai naji gawwww hannuna ya hade da fanka ,wlh lokacin nayi tunanin hannun ya cire amma ina dubawa sai naga yankar ba wata babba bace, Allah ya tsare

Kara karanta wannan

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

Auwalu Abdullahi:

Allah ya kiyaye. Matsalar mu idan muka saka fankar sama mantawa muke da duba lafiyar ta da yi mata service koda sau ɗaya ne a shekara

Salma Deen:

"Wallahi nima fankar falona haka ta fado amma ALLAH ya rufa mana asiri babu wanda tasamu kuma yaran na nan a falon suna wasa dan ma guje guje sukeyi wallahi
Amma Wallahi yanzun inajin tsoron fanka sama sosai"

Rasheedat Abdallah:

"Toh Allah yakiyaye gaba Kuma Allah yamana tsari Amma wlh banama iya kwanci saina saita dashi Zan kwanta Koh Akan gado Koh falo yanzun da hknma gani saiti dashi Allah yamana tsari da munanan qaddarori."

Asali: Legit.ng

Online view pixel