Farashin Kalanzir ya yi tashin gwauron zabi, ya karu cikin jerin wahalhalun yan Najeriya

Farashin Kalanzir ya yi tashin gwauron zabi, ya karu cikin jerin wahalhalun yan Najeriya

  • Yayin da Najeriya ke fama da wahalhalu kala daban-daban, Farashin Kalanzir ya yi tashin gwauron zabo, ya kara jefa ƙasa cikin kakanikayi
  • Bincike ya nuna cewa farashin da ke ƙasa da N400 a watan Janairu, yanzun ya koma kusan N600 a kowace Lita
  • Gwamnatin tarayya ta ce tana iyakacin bakin kokarinta wajen shawo kan lamarin, wanda ya samo asali daga rikicin Rasha-Ukraine

Abuja - Duk da gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin lamarin wutar lantarki zai zama tarihi, har yanzun dai jiya a yau, 2,312MW a karshen makon nan, ba abinda ya ƙaru.

Farashin Kalanzir da Magidanta ke amfani da shi ya yi tashin da ba'a yi tsammani ba da kashi 41.4% ya koma kusan N600 a kowace Lita ɗaya, hakan ya ƙara jefa ƙasa cikin wahalhalu.

Kara karanta wannan

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A baya farashin Kalanzir na ƙasa da N400 mako biyu da suka shuɗe, yayin da a yanzu Farashin Man Fetur da Man Jirgi ya kai kusan N800 a kowace Lita ɗaya.

A wani bincike da Vanguard ta gudanar jiya da yammaci, na'urorin samar da lantarki 13 ne kacal ke kan ganiyarsu, amma baki ɗaya sauran na aiki ƙasa da yadda ya kamata.

Layin Sayen Kalanzir
Farashin Kalanzir ya yi tashin gwauron zabi, ya karu cikin jerin wahalhalun yan Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tashar samar da wuta ta Azura-Edo ita ce kan gaba a rahoto da NSO ta ƙasa ta fitar, wadda ke samar da 420MW.

Sauran tashoshin suna samar da, Geregu (Gas) - 399MW; Jebba Hydro - 334MW; Shiroro Hydro - 292MW; Sapele NIPP - 169.40MW; Omotosho (Gas) - 121MW; Omotosho NIPP - 102.50MWS, da sauran su.

A ɓangaren rarraba wutar kuwa kamfanin rarraba wutar Lantarki na Ibadan shi ke kan gaba, mai bukatar 373.69MW, Abuja na take masa baya da 312MW, sai kuma na Benin 244.17MW.

Kara karanta wannan

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

Da take jawabi kan halin da ake ciki, ƙungiyar kamfanonin samar da wutar Lantarki, APGC, ta ɗora laifin lamarin kan ƙarancin biyan kamfanonin samar da wuta.

Farashin Kalanzir ya tashi

Duk da tsoma hannun gwamnatin tarayya domin shawo kan lamarin, Farashin Kalanzir HHK, ya tashi matuƙa zuwa N600 a kowace Lita guda.

Wannan cigaban ya shafi Magidanta da dama musamman waɗan da ke zuane a yankunan karkara, kasancewar Kalanzir ne babban Man da suke amfani da shi wajen girka Abinci.

Alal misali a wani bincike da aka gudanar Farashin Kalanzir a sassan jihohin Anambra, Kano, Abia, Kaduna, Ebonyi, Ogun, Cross River ya kasance ƙasa da N400 a Lita ɗaya, amma yanzun ya kai N600.

Ba'a samar da shi a cikin ƙasa

Bayanai sun nuna cewa kamfanin mai na ƙasa NNPC bai iya samar da wani tataccen Mai ba a watan Fabrairu, da kuma watanni 12 da suka shuɗe.

A cewar NNPC hakan ya faru ne saboda gyaran da gwamnati ke cigaba da yi a Matatun mai na ƙasar nan guda huɗu.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

Rahoton NBS

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, a rahoton bincike kan Farashin Kalanzir na watan Fabrairu, 2022 da ta fitar ta bayyana cewa:

"Farashin Kalanzir na magidanta da masu amfani da shi suka biya ya tsaya a N450.66 daga N437.11 a watan Janairu, hakan ya nuna an samu ƙarin kashi 3.10 cikin 100."
"Alkaluman shekara bayan shekara sun nuna cewa an samu ƙarin ƙashi 26.66% daga farashinsa na N355.80 a watan Fabrairu, 2021."

A watan Fabrairu 2022, Matsakaicin Farashin Kalanzir a jihohin Ebonyi, Cross River da Osun ya kasance N607.14, N593.75 da kuma N531.77 a jere, yayin da jihohin Bayelsa, Jigawa da Sokoto farashin ya tsaya a N290.44, N326.39 da N340.14.

Rahoton NBS ya ƙara da cewa: "Farashin Galan ɗin Kalanzir a watan Fabrairu, 2022 ya ƙaru zuwa N1559.78 daga N1528.74 a watan Janairu, ya ƙaru da kaso 2.03 daga wata zuwa wata."

"Daga shekara zuwa Shekara kuma matsakaicin Farashin Galan ɗin Kalanzir ya ƙaru da kashi 26.46 daga N1214.24 a watan Fabrairu, 2021."

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

FG ta shiga lamarin

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar hukunta duk wani ɗan kasuwa da ta kama yana siyar da abubuwan da ake samu daga ɗanyen mai sama da farashin da ƙasa ta ƙayyade.

Ƙaramin Ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, da yake jawabi ga manema labarai a ƙarshen mako, ya ce gwamnati na kokarin kawo ƙarshen waɗan nan matsalolin.

Ya ce:

"Muna da masaniya, kamar yadda kuka ji shugaba Buhari ya faɗa a wani jawabi, wasu yan kasuwa na amfani da halin da ake ciki wajen ƙara farashin kayayyakin."
"Ina mai tabbatar muku da cewa mun tanadi hukunci kan irin waɗan nan bara gurbi. Zamu ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda ke kokarin ƙara tsananta wa halin da mutane ke ciki yanzu."
"Mun shiga mawuyacin hali a yan makonnin nan, matsalar karancin Fetur wacce muka magance kasancewar ta jingina da mamayar Rasha a Ukraniya. Yan Najeriya na shan wahala saboda tashin farashin Fetur wanda ke faruwa a faɗin duniya, ba wai mu kaɗai abin ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Kwara, Ɗan a mutun Bukola Saraki ya sauya sheka zuwa APC

Jam'iyyar PDP ta ɗauki matakin dakatarwa kan tsohon kwamishinan ilimi kuma ɗan amutun Saraki, Injiniya Musa Yeketi.

Sai dai bayan faruwar haka, Misata Yeketi, ya bayyana ficewarsa daga PDP, tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel