JAMB: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Mafi Ƙarancin Shekarun Shiga Jami'a a Najeriya

JAMB: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Mafi Ƙarancin Shekarun Shiga Jami'a a Najeriya

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta fara shirin aiwatar da shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a a Najeriya
  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce a yanzu za ka ga ɗalibai ƴan shekara 15 da 16 suna zana jarabawar JAMB
  • Farfesan ya kuma yi kira ga iyaye da su bar ƴaƴansu su kai matakin mallakar hankali gabannin su tura su jami'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta koƙa kan ƙaruwar yara masu kananan shekaru a jami'o'in Najeriya.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, shi ne ya nuna damuwa kan lamarin yayin da yake zagayawa domin duba yadda jarabawar share fagen shiga jami'o'i (UTME) ke gudana a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Farfesa tare da sace mutum 2 a wani sabon hari

Ministan ilimi, Tahir Mamman.
UTME: Gwamnatin Tinubu za ta aiwatar da mafi ƙarancin shiga jami'o'i a Najeriya Hoto: Prof. Tahir Mamman
Asali: Twitter

Minista ya ziyarci masu jarrabawar JAMB

Farfesa Mamman ya ce gwamnati na shirin yin nazari tare da sanya shekaru 18 a matsayin mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ma'aikatar ilimi ta ankara da shekarun ɗaliban da ke neman gurbin shiga jami'o'i kuma galibi sun yi ƙanƙanta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan ya ce:

"Mun lura da shekarun wadanda suka nemi gurbin shiga jami’a, wasu daga cikinsu sun yi kanana sosai. Zamu sake nazari domin sun yi kanana su fahimci ilimin jami'a."
"Wannan mataki ne da ɗalibai ke zuwa wurin da suke da alhakin kula da dukkan harkokinsu saboda haka idan ba su girma ba, ba zasu iya yin abin da ya kamata ba.

Gwamnati ta faɗi mafi ƙarancin shekarun jami'a

Farfesa Mamman ya ƙara da cewa a yanzu akwai ɗalibai ƴan shekara 15 ko 16 da zana jarabawar JAMB, inda ya yi kira ga iyaye su daina tura ƴaƴansu matakin da ya fi ƙarfinsu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mazauna kauyen Zamfara sun nemi mafaka a gidan gwamnati

"Za mu duba wannan lamarin domin 18 ne shekarun shiga jami'a amma za ka ga dalibai ƴan ahekara 15 ko 16 suna zuwa jarrabawar JAMB. Ba abu ne mai kyau ba.

Ministan ya bukaci iyaye da su bar ‘ya’yansu su mallaki hankali kafin su shiga jami’a domin su samu damar tafiyar da al’amuransu yadda ya kamata, This Day ta ruwaito.

Ɗaliban da suka fi cin makin JAMB

A wani rahoton kuma Kamfanin tattara alkaluma ta StatiSense ta fitar da jerengiyar dalibai da suka fi kowa kokari a jarrabawar JAMB cikin shekaru 10 da suka wuce.

Kididdigar da ta fara daga shekarar 2014 zuwa 2023 ta fitar da daliba mace ce a matsayin wacce ta fi kowa kokari yayin da na miji ke bi mata baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel