Yanzu-Yanzu: Jerin kudurori 8 da suka tsallaka karatun farko a zauren majalisar wakilai

Yanzu-Yanzu: Jerin kudurori 8 da suka tsallaka karatun farko a zauren majalisar wakilai

  • Wasu kudurori guda takwas sun tsallaka karatu na farko a zauren majalisar wakilai
  • Majalisar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Maris
  • Daga cikin kudurorin harda na gyara dokar hukumar jarrabawar JAMB

Abuja - Wasu kudurori takwas sun tsallaka karatun farko a zauren majalisar wakilai a ranar Laraba, 16 ga watan Maris.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na Twitter inda ta jero kudirorin da suka tsallake wannan matakin.

Majalisar ta kuma bayyana mambobinta da suka dauki nauyin kudirorin a matsayin; Hon. Mohammed Saidu Bargaja, Hon. Musa Agah Avia, Hon. Toluope Akande Sadipe, da kuma Hon. Olusola Steve Fatoba.

Yanzu-Yanzu: Jerin kudurori 8 da suka tsallaka karatu na farko a zauren majalisar wakilai
Yanzu-Yanzu: Jerin kudurori 8 da suka tsallaka karatu na farko a zauren majalisar wakilai Hpoto HouseNGR
Asali: Twitter

Kudurorin sune:

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Alkalin kotun Abuja ya shiga jerin wadanda ake tuhuma da rashin da'a

1. Kudirin dokar kafa jami’ar tarayya ta noma, Mpu, jihar Enugu, 2022

2. Kudirin dokar kafa kwalejin tarayya, Sabon Birni Gobir, jihar Sokoto, 2022 (HB. 1899).

3. Kudirin dokar kafa cibiyar lafiya ta tarayya, Isa, jihar Sokoto, 2022 (HB. 1990).

4. Kudirin dokar kafa kwalejin ilimi ta tarayya (Fasaha) Kwal, jihar Plateau, 2022 (HB. 1991)

5. Kudirin dokar kafa cibiyar lafiya ta tarayya, Kissaloi, jihar Plateau, 2022 (HB. 1902)

6. Kudirin dokar gyara a dokar hukumar jarrabawar JAMB, 2022 (HB. 1903)

7. Kudirin dokar kafa kwalejin ma’aikatan jinya da unguwar zoma, Ado-Ekiti, jihar Ekiti, , 2022 (HB. 1904)

8. Kudirin dokar kafa ma’aikatar bincike da sarrafa shinkafa ta kasa, Igbemo, jihar Ekiti, 2022 (HB. 1905).

Majalisar Dattawa ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da kafa makarantar koyar da ilimin ma'adanan ƙasa da ilimin halitta a Guyuk.

Kara karanta wannan

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC

Haka nan kuma majalisar ta amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha (Poly) Offa, jihar Kwara, daga mai bada Diploma zuwa Jami'a mai bada takardar shaidar kammala Digiri.

Sannan kuma majalisar ta sake amincewa da kudirin jami'o'in fasaha na tarayyan Najeriya 2004 wanda ta yi wa garambawul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel