Daga yanzu mutum ko alamun Malaria yake da shi kawai Korona ne, gwamnan Legas
- Gwamnan Legas ya nuna alhininsa kan yawaitan sabbin masu kamuwa da Korona
- Daga yanzu, gwamna Sanwo Olu ya bukaci duk mai jin zazzabi ya je ayi masa gwaji
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira ga mutan jiharsa cewa daga yanzu a rika daukan alamun zazzabin cizon sauro a matsayin Korona har sai gwaji ya nuna sabanin haka.
Gwamnan ya bayyana hakan ranar Talata yayin hira da manema labarai kan inda aka kwana wajen yaki da cutar COVID-19, musamman yadda adadin masu kamuwa kullum ke karuwa.
Saboda haka, ya shawarci duk wanda ya ke ganin alamun zazzabin cizon tsauro a jikinsa ya garzaya wuraren gwajin Korona domin yi musu gwaji kyauta saboda a cewarsa "neman lafiya na wuri na da muhimmanci ga rayuwar mutum idan ta tsananta."
Gwamna Sanwo-Olu ya kara da cewa akwai muhimmanci mutan jihar su koyi dabi'ar bin dokokin kiyaye kai da hana yaduwar cutar saboda hakan zai taimakawa gwamnati wajen kokarin dakile cutar.
A cewar gwamnan, wannan waiwaye na Korona ta biyu ya zo da kalubalen bukatuwar iskar Oxygen ga marasa lafiya a fadin tarayya.
KU DUBA: Gwamnatin tarayya ta shirya tallafawa yara 10m da ba sa makaranta
KU KARANTA: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG
A wani labarin kuwa, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce kawo yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yanzu ya zarce 112,000 cikin samfuri milyan 10 da aka gwada.
Mutane 1,301 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 18 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 113,3015 a Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng