Bidiyon adaidaitan Bakano da ya kawata ta da TV, kafet da sifikar sauti ya kayatar

Bidiyon adaidaitan Bakano da ya kawata ta da TV, kafet da sifikar sauti ya kayatar

  • Wani matukin adaidaita a jihar Kano ya dauka hankalin masu amfani da yanar gizo, bisa yadda ya kayata adaidaitar shi
  • An gani a wani bidiyo yadda kayatattar adaidaitar take dauke da karamin talabijin, kafet da kayan kida na zamani
  • Keken adaidaita sahun ta kunshi duk wasu ababen more rayuwa da zai sa kwastomomi jindadin tafiyar ta su

Kano - Wani mutumi dan Najeriya mai kayatacciyar adaidaita sahu, wacce ta sha bambam da sauran ya bar masu amfani da kafar sada zumuntar zamani cikin tsananin mamaki.

An ga mutumin a jihar Kano a wani bidiyo da ake da tabbacin wani daga cikin kwastomomin shi ne ya mishi.

Bidiyon adaidaitan Bakano da ya kawata ta da TV, kafet da sifikar sauti ya kayatar
Bidiyon adaidaitan Bakano da ya kawata ta da TV, kafet da sifikar sauti ya kayatar. Hoto daga @saintavenue_ent1
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

A tsokacin da @saintavenue_ent1, wanda ya wallafa bidiyon a Instagram yayi karkashin bidiyon na nuna yadda keken ke da kafet, kayan sauti da talabijin a ciki.

Alamu sun nuna cewa an yi gyare-gyaren da karin don bawa fasinjoji more rayuwar da ba za su taba mancewa ba, duba da irin fasaha da basirar direban.

Ga wasu daga cikin tsokacin masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani:

@ruchie-stoner02 ya ce: "Wahala."
@shes-spotless ta tofa nata albarkacin: "Jindadi."

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

A wani labari na daban, a kwanakin baya jaruma Rukayya Dawayya ta fara gina wani tamfatsetsen gida a Kano wanda da ganinsa ka san an yi barin miliyoyin naira wajen gina shi.

Tun ana tsaka da ginin gidan ta wallafa a shafinta na Instagram inda abokan sana'arta suka dinga taya ta murna da fatan kammalawa lafiya.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

A halin yanzu dai wannan katafaren gida ya kammalu inda ta sake wallafa bidiyon ciki da wajensa a shafinta na Instagram tare da mika godiya ga Allah da ya bata ikon kammala ginin nata.

Sai dai ko da jarumar ta wallafa bidiyon a shafinta, babu jimawa ta goge wanda za ta yuwu hakan ya na da alaka da irin maganganun da za ta iya samu a sashin tsokaci ne.

Legit.ng ta lalubo muku bidiyon daga shafin masana'antar a Instagram inda aka wallafa tare da taya ta murna.

A cikin kwanakin nan an dinga kai ruwa rana da matan masana'antar bayan jaruma Ladin Cima ta bayyana cewa dubu biyu zuwa dubu biyar ake biyansu wurin daukar fim.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel