Katsina: 'Yan Sanda Sun Kama Wata Hajiya Fatima Da Ke Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Layyu Da Leƙen Asiri

Katsina: 'Yan Sanda Sun Kama Wata Hajiya Fatima Da Ke Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Layyu Da Leƙen Asiri

  • Yan sandan Jihar Katsina sun yi nasarar kama wata Hajiya Fatima Alhaji, mai shekaru 35 da ake zargin tana aiki da yan bindiga
  • SP Gambo Isah, kakakin yan sandan Jihar Katsina ya ce ana zargin tana samarwa yan ta'addan asiri kuma tana musu aikin leken asirin mutanen gari
  • Wacce ake zargin ta amsa cewa tana kai wa wani hatsabibin shugaban yan ta'adda, Sani Mohidinge, layyu da bayanai game da mutanen gari

Jihar Katsina - Yan sanda a Jihar Katsina sun kama wata mata mai shekaru 35, Hajiya Fatima Alhaji, da ake zargi tana yi wa yan bindigan da ke addabar jihar da kewaye asiri.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gamba Isah ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa an kuma gano cewa Fatima yar leken asirin ya bindiga ne, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

Katsina: 'Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Da Ke Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Layyu Da Leƙen Asiri
Katsina: An Kama Wata Mata Da Ke Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Layyu Da Leƙen Asiri. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ya ce yan sandan sun kama Fatima mazauniyar Dajin Daha a karamar hukumar Danmusa na jihar a ranar 13 ga watan Fabrairu bayan samun bayyanan sirri.

"Tana taimaka musu, tana kai wa yan bindigan da ke adabar jihar da kewaye bayanai sannan tana samar musu layyu da asiri.
"A yayin bincike, an gano wasu layyu daga gidan wacce ake zargin da ake kyautata zaton yan bindiga ke amfani da su don kai hari.
"Wacce ake zargin ta amsa cewa tana kai wa wani Sani Mohidinge, hatsabibin shugaban yan bindiga da ake dade ana nema magunguna," in ji shi.

Yan sandan sun kuma kama yan bindiga uku

Yan sandan sun kuma yi nasarar kama wasu mutane uku; Shamsudeen Dahiru, 35, Bala Inuwa, 35 mazauna Funtua da wani Jamilu Isah, 35, mazaunin Kofar Marusa Quaters, Katsina, kan garkuwa da ta'addanci.

Kara karanta wannan

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

Sun kware wurin kai wa yan ta'adda bayanai a daji da kuma yi wa yan ta'adda jagora zuwa kauyuka idan za su kai hari ko garkuwa kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Dahiru ya amsa cewa motarsa ne aka yi amfani da ita wurin sace wani Alhaji Sule na kauyen Dankawuri a karamar hukumar Matazu a jihar.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel