Gobarar sansanin 'yan gudun hijira: Zulum ya kai ziyara, ya nemi a lissafa gidajen da suka lalace

Gobarar sansanin 'yan gudun hijira: Zulum ya kai ziyara, ya nemi a lissafa gidajen da suka lalace

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ziyarci sansanin yan gudun hijira na Muna Elbadawy da ya kama gobara
  • Zulum ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) da ta lissafa tare da mika bayanai kan adadin gidajen da gobara ya shafa domin gwamnatin jihar ta tallafa
  • Ya kai ziyarar ne a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, inda ya zagaya wajen da annobar ta afku

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) da ta lissafa tare da mika bayanai kan adadin gidajen da gobara ya shafa domin gwamnatin jihar ta bayar da agaji yadda ya kamata.

Zulum ya bayar da umurnin ne a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, yayin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da gobara ta cika da su a sansanin yan gudun hijira na Muna Elbadawy, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da sanarwa.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kejerar ministan mai, ta fadi dalili

Gobarar sansanin 'yan gudun hijira: Zulum ya kai ziyara, ya nemi a lissafa gidajen da suka lalace
Gobarar sansanin 'yan gudun hijira: Zulum ya kai ziyara, ya nemi a lissafa gidajen da suka lalace Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Gobarar wacce ta tashi a sansanin yan gudun hijirar da ke wajen Maiduguri, ya halaka rai daya sannan ya jikkata mutane 17 yayin da ya halaka matsuguni sama da guda 100. Sansanin na dauke da gidaje fiye da 10,000 da mutane 50,000.

Gwamnan ya kuma sanar da cewar gwamnatin jihar na duba yiwuwar hada hannu da gwamnatin tarayya da hukumomin agaji domin mayar da su da sauran yan gudun hijira da ke Maiduguri da kewaye zuwa gidajensu ko garuruwa mafi kusa irin su Ngwom da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya yi korafin cewa da dama basu fahimci dalilin da yasa gwamnatin jihar Borno ke kokarin mayar da yan gudun hijira tushensu ba. Ya bayyana cewa babu lokacin da gwamnatin jihar ta tursasa yan gudun hijira komawa gidajensu.

Da yake misali da mummunan yanayin da suke ciki, yanayin tsafta, rashin matsuguni mai kyau da cunkoso, duk da cewa sansanin ba na hukuma ba ne, don haka akwai bukatar a sake matsuguni cikin mutunci.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

Gwamnan ya ci gaba da bayanin cewa sauya masu muhalli zai basu damar sake gina rayuwarsu da kuma basu damar kula da tarbiyar yaransu yadda ya kamata.

Jagoran NEMA (Arewa maso gabas), Usman Mohammad Aji da Darakta Janar na SEMA ta jihar Borno, Hajiya Yabawa Kolo sun korawa Gamna Zulum bayani sannan suka zagaya da shi wajen a yayin ziyarar.

Shugaban NEMA ya sanar da gwamnan cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1:00 na rana daga daya daga cikin lemomin da ke sansanin da daya daga cikinsu ke dafa abinci. Sai dai jami'an hukumar kashe gobara ta jihar sun shawo kan lamarin.

Gobara ta yi kaca-kaca da sansanin 'yan gudun hijira a Borno

A baya mun kawo cewa wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da yankin Muna a karamar hukumar Jere a jihar Borno dake Arewa maso Gabas ya kone kurmus a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci

A gefe guda, gwamnan jihar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum tare da Sanata Kashim Shettima sun ziyarci garin Gamboru da ke karamar hukumar Ngala daga ranar Lahadi zuwa Talata.

Shugabannin sun duba tare da shiga cikin masu raba kayan abinci da sauran kayan tallafi ga mutane 60,813 masu gudun hijira da wadanda suka koma yankin.

Wadanda suka mori tallafin sun hada da mata 39,903 da suka samu tallafin N5,000 da zannuwa da maza 15,350 maza da suka samu tallafin shinkafa da masara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel