Da dumi-dumi: Gwamna ya nada tsohon sanata matsayin sarkin gargajiya a jiharsa

Da dumi-dumi: Gwamna ya nada tsohon sanata matsayin sarkin gargajiya a jiharsa

  • Gwamnan jihar Oyo ya amince da nada Sanata Lekan Balogun a matsayin sarkin gargajiya a jihar ta Oyo
  • Ya amince da nadin nasa ne bayan da ya karbi takardar shawarar daga masu fada aji a nadin saurauta a masarautar jihar
  • Wannan ya faru ne bayan rusa wata dokar da aka kawo na cewa, dole a zabi sarkin ba wai nada shi ba kai tsaye

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya amince da nadin Sanata Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 na Ibadanland.

Amincewar ya biyo bayan shawarar da majalisar masarautar Olubadan ta yanke kuma ta sanar da Gwamnan, inji rahoton The Nation.

Gwamna Makinde na jihar Oyo ya yi nadin sarauta
Da dumi-dumi: Gwamna ya nada sarkin gargajiya a jiharsa bayan mutuwar na baya | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Makinde ya bayyana hakan ne a wajen jana’izar marigayi Olubadan Saliu Adetunji a karshen mako.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaransa, Mista Taiwo Adisa, ya yi wa sabon Olubadan fatan samun nasarar gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makinde ya ce:

“Na yi farin cikin sanar da nadin Otun Olubadan na Ibadanland, Babban Basarake Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 na Ibadanland.
“Nadin ya yi daidai da shawarar majalisar masarautar Olubadan na Ibadan, da kuma al’adun mutanenmu na musamman da aka gwada a kan lokaci.
"A madadin gwamnati da mutanen jihar Oyo, ina yiwa sabon Olubadan fatan samun nasarar mulki mai albarka da zaman lafiya da cigaban da ba a taba samu ba."

An soke batun yin zabe

Gwamnan ya kuma amince da soke shawarar masarautar Ibadan da aka yi wa kwaskwarima, wadda ta tsara zabe ga kujerar sarautar Olubadan na Ibadan, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya ɓarke tsakanin mambobin NURTW

Sanarwar ta nuna cewa Gwamnan ya bayar da umarnin soke zaben ne a ranar 11 ga Fabrairu, 2022, bisa ga ikon da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya ba shi, 1999,

Duba da haka Babbar kotu a jihar a ranar 1 da 10 ga Fabrairu karkashin sashe na 7, 20,26 da 30 na dokar sarakunan jihar Oyo na shekarar 2000 ta soke batun.

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya rika gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

A wani labarin, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Kara karanta wannan

Tazarce: An bawa gwamna kyautar takobi, bammi, taburma da wasu kayayyaki a jiharsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel