Tazarce: An bawa gwamna kyautar takobi, bammi, taburma da wasu kayayyaki a jiharsa

Tazarce: An bawa gwamna kyautar takobi, bammi, taburma da wasu kayayyaki a jiharsa

  • Shugabannin jam'iyyar APC da na gargajiya sun bawa Gwamna Adegboyega Oyetola kyautan takobi, banmi, taburma da ruwa daga rafin Oluminrin
  • Sun bawa gwamnan wadannan kayayyakin na al'adun mutanen Ijesa ne domin nuna goyon bayansu ga tazarcen da gwamnan ke son yi a zabe da ke tafe a jihar
  • Gwamna Oyetola ya yi godiya bisa kyautar da suka masa sannan ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar APC su fita su sanar da mutane irin nasarori da ayyukan da gwamnatinsa ta yi

Osun - A ranar Laraba, Shugabannin jam'iyyar APC sun bawa gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola kyautan takobi, banmi, taburma da ruwa daga rafin Oluminrin a matsayin alama ta goyon bayansa ya yi tazarce.

Shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin Desmond Ojo, dan majalisar jiha mai wakiltar Oriade, ya ce kyaututukan da aka bawa gwamnan alama ce ta al'adun mutanen Ijesa, The Punch ta ruwaito.

Tazarce: An bawa gwamna kyautar takobi, bammi, taburma da wasu kayayyaki a jiharsa
Tazarce: An bawa Gwamna Oyetola kyautar takobi, bammi, taburma da wasu kayayyaki a Osun. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

An gabatarwa gwamnan da tawagarsa wannan kyaututukan ne a dakin taro na Ijebu Jesa inda aka yi amfani da kayayyakin aka yi wa Oyetola addu'ar samun nasara a zaben gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin jawabin da ya yi wa shugabannin gargajiyar da na APC da suka hallarci taron, Oyetola ya mika godiyarsa ga sarakunan gargajiyan bisa juriyarsu.

Yayin da ya ke karbar kayayyakin da suka bashi kyauta, ya ce:

"Na yarda da amfanin takobi a matsayinsa na alama ta nasara, cin galaba da sa'a."

Ya kuma bukaci magoya bayan jam'iyyar su fara bayyanawa al'umma irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi, su kuma goyi bayan jam'iyyar mai mulki.

Sarakuna sun nuna gamsuwarsu bisa kamun ludayin gwamnatin Oyetola

Sanarwar da ta fito daga Sakataren Watsa Labarai na gwamnan, Ismail Omipidan, ta kuma ce Alademure na Ibokun, Oba Festus Awogboro, yayin jawabin da ya yi wa tawagar gwamnan a Ibokun, ya bukaci kada su bari a janye hankalinsu daga ayyukan da suke yi.

Hakazalika, Elegboro na Ijebu-Jesa, Oba Moses Agunsoye, ya nuna gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da mulki a jihar, rahoton The Punch.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel